Rundunar ‘yansanda a Jihar Adamawa ta kama wani matashi dan shekara 20 da ake zargin dan fashi ne mai suna Abubakar Abdu, da laifin daba wa wata mata wuka har lahira a lokacin da yake yunkurin yi mata fashin masara.
Lamarin, a cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Suleiman Nguroje ya fitar a kauyen Gengle da ke Karamar Hukumar Mayo Belwa a jihar.
- Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Kolin CEO Na APEC
- Mizanin Hajoji Da Hidimomi Da Masana’antun Kasar Sin Ke Samarwa Ya Karu Da Kaso 5.3 Bisa Dari A Watan Oktoba
Ya kara da cewa wanda ake zargin ya shiga gidan wanda abin ya shafa ne domin ya sace masara mai yawa amma sai matar gane kuma ta yi masa ihu.
Da jama’a suka farga sai wanda ake zargi ya yi yunkurin guduwa inda ya yi nasarar daba wa matar wuka a kokarin tserewa daga wurin da lamarin ya faru.
An ce tasirin raunukan da aka samu daga harin wuka da aka kai ya yi sanadiyyar mutuwar wanda aka kashe.
PPRO ta bayyana cewa, “A ranar 10 ga Nuwamba, 2024, rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa a yaki da munanan laifuka ta cafke wani matashi mai suna Abubakar Abdu mai shekaru 20, mazaunin kauyen Gengle na Karamar Hukumar Mayo Belwa bisa laifin kashe wata mata Azumi Abubakar mai shekara shekara 30 da wuka har lahira.
“Wanda ake zargin ya kai hari ne a ranar 7/11/2024 da misalin karfe 3:00 na dare ya shiga gidan Azumi ya saci masara da dama. A kokarin tserewa ne, sai Azumi ta ganshii, ta kuma kira sunan wanda ake zargin. Da ya fahimci an gane shi, nan take ya far wa Azumi ta hanyar daba mata wuka wanda a sakamakon haka ta mutu.”
Ya kara da cewa za a gurfanar da Abdu a gaban kotu bayan kammala binciken da ake yi.
“Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike,” in ji Nguroje.