Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke jami’in da aka damkawa tallafin manoman auduga da bankin Najeriya ta bayar a wani yankin Neja. Lamarin ya faru ne bayan shugabannin kungiyar manoman auduga ta nada wasu shugabannin shiyya da zasu kula da baiwa manoman da aka tantance dan baiwa tallafin.
Da yake karin haske ga manema labarai, sakataren kungiyar ta jiha, Ambasada Nura Hashim, yace bayan wa’adin da babban bankin Najeriya ta bayar na kammala raba kayan ga manoman da aka tantance, matakin shugabancin jiha ta nada kwamitocin da zasu kula da mutanen yankunan su.
Bayan mun tantance sunayen mun baiwa kowa aikin da zai yi, sai muka samu labarin yadda ake rabon kayan a wani yankin wanda ba mu lamunci hakan ba, bayan mun yi bincike sai muka samu labarin an karkatar da rabin kayan wanda mu ba mu san inda aka yi da kayan ba.
Jin hakan na sanar shugaban kungiya ta jiha, nan take ya ba ni damar daukar matakin da ya dace, jin haka kuma na sanar da uwar kungiya ta kasa dan ta san abinda ke faruwa inda ta ba ni damar baiwa jami’an ”yan sandar yankin damar cafke shi.
Zuwa yanzu bayan an kama shi ya amsa laifin sa kuma ya bayyana inda kayan suke, wanda mun karbe aikin a hannunsa kuma za mu sanya idanu dan tabbatar da cewar kowani shiyya an yi aikin yadda ya kamata.
Da farko mun ce a baiwa kowani manomi buhun taki biyar, maganin feshi guda biyu da injimin feshin ga kowani manomi, amma sai mu ka ji labarin ba haka ake rabon ba, alhalin duk wanda aka baiwa kayan zai biya, bayan mun cafke shi an dawo da kayan da aka karkatar duk da cewar an nemi mu sakaya sunansa maganar ba wadda za mu yi shiru ba ne dole mu bayyana wa duniya domin wanda ke tunanin irin wannan halin yasan cewar muna kallon kowa.
Wannan ya ba mu damar, za mu ziyarci gonakin manoman dan ganin irin kalubalen da su ke fuskanta kafin shukar audugar da bayan shuka har zuwa cirewa.
Yanzu maganar da mu ke yi da ku mun zauna da sarakunan yankin dan cigaba da baiwa manoman kayansu.