Jami’an tsaro sun kama Yahaya Zango, wanda ake zargi da garkuwa da mutane a sansanin alhazai na babban birnin tarayya Abuja a ya yin tantance alhazan da za su tashi zuwa Æ™asa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar jami’an tsaro a sansanin alhazan ne suka tabbatar da cafke Yahaya Zango, wanda ya taso a unguwar Paikon-Kore a Æ™aramar hukumar Gwagwalada da ke babban birnin tarayya Abuja.
- NDLEA Ta Kama Masu Sayar Da Kwaya Ga Ƴan Bindiga A Kano
- Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa
Jami’an tsaro sun dai bayyana shi a matsayin wanda suke nema ruwa a jallo a baya, sakamakon zargin da ake masa na hannu a garkuwa da mutane da aka yi da dama.
“Da yammacin wannan rana ne jami’an tsaro na farin kaya suka cafke shi a lokacin da ake tantance alhazai a sansanin alhaza a filin jirgi a Abuja” kamar yadda majiya ta bayyana.
Yahaya Zango dai ya nuna katin fasfo É—insa sannan ya bi layi tare da sauran alhazai kafin jami’an tsaro na farin kaya su ganshi sannan su cafke shi.
Wani babban jami’in hukumar jin daÉ—in alhazai ta babban birnin tarayya Abuja wanda ya buÆ™aci a sakaya sunansa ya tabbatar da cafke Yahaya Zango inda ya ce ya daÉ—e yana wasan É“uya tsakaninsa da jami’an tsaro kafin dubunsa ta cika a yau.
“Ya so ya shige cikin sauran alhazai amma tuni jami’an tsaro sun gama shirya kama shi” a cewar jami’in.
Har kawo yanzu dai jami’an tsaro na farin kaya ba su ce komai ba game da kamen da suka yi.
Nigeria dai tana fama da matsalar rashin tsaro na masu garkuwa da mutane da Æ´an bindiga musamman a yankin Arewa ta tsakiya da Arewa maso yamma. Duk da yunÆ™urin da jami’an tsaro suke yi amma har yanzu matsalar tsaron tana ciwa gwamnati tuwo a Æ™warya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp