A ranar Talatar da ta gabata ne aka gurfanar da wasu mutum uku a shalkwatar ‘yan sandan Jihar Osun da ake zargi a harin da aka kai a wata Cocin Celestial da ke kauyen Odu kusa da Osogbo.
An cafke wadanda ake zargin sun kai hari cocin ne a lokacin da suke sintiri da sanyin safiyar Talata.
- Rikicin Nijar: Tinubu Ya Aika Janar Abdulsalami, Sultan Na Sokoto Zuwa Yamai
- Me Ya Haifar Da Koma Bayan Ababen More Rayuwa A Kasar Amurka?
A yayin harin, wadanda suka kai harin sun yi awon gaba da mabiya cocin 12, amma wadanda abin ya shafa sun gudu daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su a lokacin da suka ci karo da wasu mafarauta da kuma wasu masu aikin sa kai na yankin da aka kira su suka zo cikin gaggawa.
A yayin faruwar lamarin, an ruwaito cewa wadanda suka aikata laifin sun yi wa wata ‘yar cocin fyade wacca ba a bayyana sunan ta ba.
Da take ba da labarin abin da ya faru, wata mawakiyar coci, wanda Fasto mai kula da cocin ya gayyace ta mai suna Esther Ayodeji, yayin wata tattaunawa da jaridar PUNCH Metro ta ce, “Na isa cocin ‘yan mintuna kadan bayan karfe 10 na dare a ranar Litinin don wasu ayyukan da suka shafi coci. Mun fara sintiri ne da tsakar dare. Bayan kammala dukkan hidima tare da masu ganguna sauran wasu mutane na cikin cocin, amma saina fita.
“Bayan ‘yan mintoci kadan, daga inda na tsaya tare da limamin cocin, muka fara jin harbe-harbe a ciki, mun shiga wani yanayi mai cike da rudani, don haka, duk sai muka gudu cikin daji. Cikin wadanda muka gudu sai muka hadu a daji mu bakwai, shida mata da namiji daya. Muna cikin yawo a cikin daji, sai ga wasu mutane biyu dauke da makamai suka bayyana a gabanmu, duk muka tarwatse da gudu wurare daban-daban”.
Wani mamba a cocin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an kai wacce aka yi wa fyaden asibiti, inda ya kara da cewa a wannan lokacin dai lamarin na su basu samu nasara ba nasara ba saboda saurin daukin mutanen kauyen da mafarauta da jami’an ‘yan sanda suka kawo.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Yemisi Opalola, wanda ya shawarci kungiyoyin addini da su guji yin shirye-shirye da yamma ko kuma safiya, musamman a cibiyoyi da ke a kebabbun wurare, ya ce ana ci gaba da yi wa mutane uku da aka kama a kusa da wurin tambayoyi.
Da yake gabatar da sauran wadanda ake zargi da suka hada da wadanda aka kama da laifin zama mambobin kungiyoyi haratattu da suka hada da fashi da makami, Opalola ya ce Adebayo Adedayo da Adeyemi Sodik sun kai wa wani dan kasuwa hari a Iragbiji inda suka sace kudi da kayayyaki da aka kiyasta sun kai kimanin Naira 877,000.
Ta kara da cewa Yusuf Baoku da Ajayi Ismail, wadanda aka kama da laifin yunkurin kisan kai da kuma zama mambobin haramtacciyar kungiya, za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp