Kamfanin jiragen sama na Ethiopia Airlines ya ce jirgin saman Nigeria Air wanda aka tafka cece-kuce a kansa zai fara zirga-zirga a watan Oktoban 2023.
LEADERSHIP ta ruwaito a baya cewa an kaddamar da sabon jirgin ne a shekarar 2018 a Landan sannan kuma aka sake kaddamar da shi a watan Mayun 2023, karkashin tsohon ministan sufurin jiragen sama na Nijeriya Hadi Sirika.
- An Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kai Hari Wani Coci A Osun
- Ba Mu Soke Lasisin ‘Yan Kannywood Domin Musguna Wa Wasu Ba – Al-Mustapha
Sai dai rahotanni sun nuna cewar kamfanin jiragen saman Ethiopian Airlines ne ya mallaki kashi 49 cikin 100 na Nigeria Air, inda gwamnatin tarayya ke da kashi biyar cikin dari, sai kashi 46 na masu zuba jari a Nijeriya.
Da yake zantawa da gidan talabijin na Bloomberg, babban jami’in hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama na Habasha, Mesfin Tasew, ya ce kamfanin zai fara aiki nan ba da jimawa ba.
Tasew ya ce, “Kamfanin jirgin zai fara aiki da jirage biyu. Muna son ganin jirgin ya fara tashi don kasuwancin cikin gida da na duniya.”
“Kamfanin jiragen Habasha ne zai kula gudanar da aikinsa. Babbar manufar ita ce a bai wa Nijeriya damar samun ‘yancin gudanar da sufurin jirage.
“Muna da kashi 49 cikin 100 na kamfanin jirgin saman, gwamnatin Nijeriya kashi biyar cikin 100, sai sauran masu zuba hannun jari na hukumomi ke da sauran.
Tasew ya bayyana kyakkyawan fatan habakar tattalin arzikin Nijeriya.
Jirgin na Nigeria Air zai fara zirga-zirga a cikin gida sannan zai fadada zuwa biranen yammacin Afirka da kuma manyan birane da suka hada da Landan, New York, da Shanghai.