Rundunar ’Yansandan Jihar Binuwe ta tabbatar da sako ɗalibai 20 daga Jami’ar Maiduguri da Jami’ar Jos waɗanda wasu ’yan bindiga suka sace a ranar 15 ga watan Agusta.
An sace ɗaliban ne a Oturkpo yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa taron ƙungiyar ɗaliban aikin Likita da na Likitancin Haƙori na ɗariƙar Katolika (FECAMDS) a Enugu, tare da wani likita da ke tare da su.
- Martani: Ba Hannu Na A Kisan Sarkin Gobir, Sharri Ne Na Ƴan Adawa – Hon Boza
- Kisan Gillar Basaraken Daular Gobir A Hannun Masu Garkuwa Ta Girgiza Al’umma
Kakakin rundunar, Uwargida Sewuese Anene, ta tabbatar da ceto ɗaliban a daren Juma’a, inda ta ce za a fitar da cikakken bayani yau Asabar. An sako ɗaliban ne bayan tura runduna ta musamman zuwa Binuwe da Sufeto-Janar na ’Yansandan Nijeriya, Olukayode Egbetokun, ya yi, da kuma sauya matsugunin Kwamishinan ’Yansandan Jihar zuwa Oturkpo.
Rahotanni sun nuna cewa haɗin gwuiwa tsakanin jami’an tsaro, ƙarƙashin jagorancin Ofishin mai ba wa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ya taimaka wajen ceto ɗaliban.