Jami’an tsaro a Jihar Kogi sun ceto mutane 21 da aka yi garkuwa da su, sa’o’i 48 bayan sace su a ranar a hanyar Ajaokuta zuwa Itobe a jihar.
Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ya yaba da kokarin jami’an tsaron, ya jaddada cewa ba za’a iya ci gaba da jure aikata miyagun laifuka a jihar ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito.
- Gwamnatin Zamfara Ta Rufe Kasuwannin Shanu 11 Saboda Matsalar ‘Yan Bindiga A Jihar
- Tsohuwar Ministar Jin Kai, Sadiya Ba Ta Ƙi Amsa Gayyatarmu Ba – EFCC
Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, Onogwu Muhammed ya fitar, ta ce tawagar hadin gwiwa ta jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sandan Nijeriya, jami’an tsaron farin kaya da ‘yan banga na yankin ne suka yi nasarar ceton.
Wadanda abin ya shafa, galibi matafiya ne, aka shiga da su wani dajin da ba a san ko ina ba a cikin dajin da ke kusa da Karamar Hukumar Ajaokuta ta Jihar Kogi.
Amma Bello da ya samu rahoton faruwar lamarin, ya ba da umarni ga jami’an tsaro da ’yan banga da su gaggauta daukar matakin kubutar da wadanda aka yi garkuwar da su tare da kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika.
“Wannan karbar umarni da suka yi ya nuna jajircewar Bello wajen tabbatar da tsaro da walwalar ‘yan kasa/mazaunan da ke karkashinsa.
“Kokarin jami’an tsaron hadin gwiwar ya samar da sakamako cikin mai kyau sa’o’i 48, wanda ya kai ga nasarar ceto mutaum 21 da aka kama.
“Bugu da kari, aikin ya kai ga cafke wasu daga cikin masu garkuwa da mutane yayin da ake ci gaba da gano wadanda ke hannunsu,” in ji sanarwar.
Bello, wanda ya yaba wa jami’an tsaro bisa gaggauwa da daukar matakan da suka dace, ya kuma jaddada muhimmancin wanzar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Kogi.
“Wannan gwamnatin ta himmatu wajen ganin ta bar wata hanya da za ta bi wajen ganin Jihar Kogi ta kasance daya daga cikin jihohin kasar nan mafi aminci.
“Ya yi amfani da damar da ya samu wajen yin gargadi ga masu mugun nufi, ya kuma gargadi masu aikata laifuka kan yin hijira zuwa Kogi domin aikata miyagun laifuka.
“Wannan ya faru ne saboda Kogi wuri ne da ba za a iya shiga a aikata kowane irin laifi ba, don haka wannan gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron jihar.
“Nasarar da aka yi ta wannan ceto ta zo ne a matsayin shaida ga hadin kai da yunkurin da jami’an tsaro ke yi a Jihar Kogi a karkashin jagorancin Bello,” in ji ta.
Ya kara da cewa sadaukar da kai na kare lafiyar ‘yan kasa, tare da tsayuwar daka wajen yaki da masu aikata laifuka, ya nuna irin sadaukarwar da gwamnati ta yi wajen samar da yanayin da mazauna yankin za su iya rayuwa ba tare da tsoro ba.