Rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna ta ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi na tsawon watanni shida daga hannun ‘yan bindiga.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin da misalin karfe 4:00 na yamma.
- NLC Ta Ki Amincewa Da Umarnin Hana Ma’aikata Saka Dogayen Kaya A Neja
- Shugaban Sin Ya Bukaci A Yi Iyakacin Kokari Wajen Ceton Mutanen Da Girgizar Kasa Ta Rutsa Da Su
Ya ce ‘yansanda sun gudanar sintiri a yankin Madachi-Galadimawa da ke karamar hukumar Zariya.
Ya ce a lokacin ne suka ci karo da wasu ‘yan bindiga wanda hakan ya sa aka yi artabu.
“Da ganin jami’an ‘yansandan, wadanda ake zargin suka gudu bayan an yi artabu, lamarin da ya sa muka yi nasarar kubutar da wani aka sace daga maboyarsu,” in ji Hassan.
“Ba tare da bata lokaci ba aka kai mutumin zuwa Asibitin kwararru na Musulmi da ke Zariya domin kula da lafiyarsa.
A yayin gudanar da bincike, an gano an yi garkuwa da mutumin a kan hanyarsa ta zuwa garin Kontagora.
Ana ci gaba da kokarin damke wadanda ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da shi.
“’Yan sanda kuma suna aiki tukuru don gano ‘yan uwan wanda abin ya shafa. Za mu yi karin bayani yayin da muka kammala bincike,” Hassan ya tabbatar.