An Ci Tarar Kano Pillars Naira Miliyan Takwas

Hukumar ‘League Management Company (LMC)’ a ranar Laraba, sun bayyana sanya wa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tarar Naira miliyan takwas bisa rikicin da ya auku a shekaranjiya Litinin wanda ake zargin akwai hannun ‘yan wasan kungiyar da magoya bayansu.

Salihu Abubakar, babban Jami’in LMC ya bayyana cewa wannan hukuncin da aka yi Kano Pillars ya biyo bayan hatsaniyar da ta auku ne ta hanyar musgunawa jami’an kula da wasan da aka buga.

An zargi ‘yan wasan kungiyar da magoya bayansu da ta da hatsaniya a yayin da kuma bayan wasa na hudu a gasar kwararrun ‘yan wasan Nijeriya wato NPFL da ya gudana a garin Legas.

“An ci Kano Pillars tarar naira miliyan 8 yayin da Kaftin din su Rabiu Ali, an dakatar da shi daga buga wasannin NPFL guda goma sha biyu.” In ji Abubakar.

An zargi magoya bayan kungiyar da shiga cikin filin da tarwatsa wadansu kayayyakin filin wasan, tare da musgunawa wadansu jami’an da suka kula da wasan da aka buga tsakanin Kano Pillars din da kungiyar Rangers wanda aka ta shi 1-1.

 

Exit mobile version