Wata babbar kotun Jihar Akwa Ibom da ke Uyo ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kaso kan wani dan acaba mai shekaru 36 bisa laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 13 fyade.
Wanda aka yankewa hukuncin, Anietie Bassey Etim, dan asalin garin Ikot Ite Udung a karamar hukumar Nsit Atai, an ce ya dauki wadda abin ya shafa a babur dinsa zuwa wata coci, inda ya yi mata fyade.
- Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azama Wajen Raya Fannin Noma
- Yanzu-Yanzu: An Sace Wasu Dalibai 4 A Ondo
Mai shari’a Gabriel Ette a hukuncin da ya yanke ya samu wanda ya yi fyaden da laifi kuma ya daure shi shekaru 20 a gidan yari.
“Za ka shafe shekaru 20 a gidan yari, bayan an same ka da laifin fyade,” cewar mai shari’a Ette.