Wata babbar kotun jihar Borno ta yanke wa Aisha Wakil, wacce aka fi sani da “Mama Boko Haram” hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari bisa samun ta da laifin zamba.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) shiyyar Maiduguri ta gurfanar da Aisha tare da Tahiru Daura da kuma Prince Shoyode a watan Satumban 2020, bisa tuhumarsu da laifuka biyu da suka hada da yaudara wajen karbar, kudin sun kai Naira Miliyan N71,400,000.
Wadanda ake tuhumar dai sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su.
Wakili da wadanda ake tuhumar, ana tuhumarsu ne da laifin zamba, wacce suka nemi Saleh Ahmad Said mai Kamfanin Shuad General Enterprises ya kawo musu buhun wanke guda 3,000 da kudin su ya kai kimanin Naira Miliyan N7,400,000.00 a shekarar 2018.
A hukuncin da kotun ta yanke a ranar Talata, Mai shari’a Aisha Kumaliya ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa wanda ake kara ba tare da wata shakka ba.
Bayan yanke hukuncin, Mai shari’a ta yanke hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zabin fansa ko biyan kudin tara ba.