Mai shari’a S. M. Shu’aibu na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, ya yanke wa wani matashi mai suna Nasiru Isa dan shekara 33 hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsa da laifin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 11.
Wani mai suna Isa, mazaunin Darmanawa Bayan Gidan Kallo a Karamar Hukumar Tarauni ta jihar, an yanke masa hukumcin aikata laifin lalata.
- Xi Zai Halarci Taron Kolin BRICS Karo Na 16 A Rasha
- Gudunmawar Da Sin Take Bayarwa Wajen Tabbatar Da Wadatar Abinci A Duniya
Alakalin kotun ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar wa da mai shari’ar ba tare da wata shakka ba, sannan kotun ta yanke wa wanda ake kara hukuncin daurin shekaru bakwai ba tare da zabin biyan tara ba.
Mai shari’a Shu’aibu ya kuma umurci mai laifin da ya biya tarar Naira miliyan 1 a matsayin diyya.
Tun da farko, hukumar hana fataucin mutane ta kasa reshen Jihar Kano, ta ce Isa ya aikata laifin ne a Unguwar Darmanawa, Karamar Hukumar Tarauni, Jihar Kano a ranar 5 ga Oktoba, 2024.
Lauyan da ya shigar da kara, Abdullahi Babale, ya ce Isa ya yaudari ‘yar makocinsa ‘yar shekara 11 ta hanyar jan ta dakin matarsa inda a nan ne ya yi lalata da ita.
“Isa ya yi lalata da yarinyar a wurare uku.
“Na daya a dakin matarsa sannan kuma biyun a wani gini da ba a kammala ba.
“Wanda aka yanke wa hukuncin ya yaudari yarinyar ne da biredi, gyada da kuma Naira 20 kafin ya yi lalata da ita,” Babale ya shaida wa kotu.
Masu gabatar da kara sun gabatar da abubuwa guda biyu, da suka hada da bayanin ikirari na wanda aka yankewa hukuncin da kuma shaidar wacce aka yi wa ta’asar, ga kotun don tabbatar da gaskiyar lamarin.
A cewar Babale, laifin da aka aikata ya ci karo da sashe na 16 (1) na dokar hana fataucin mutane (Haramci) da tilastawa mutane, ta 2015 kuma laifin yana da hukunci a karkashin sashe na 26 (1) na TIP ACT 2015.