A bisa al’ada, ana sa ran zababben Shugaban kasa, Bola Tinubu ya fara nadi mukamai bayan da Babban Alkalin-alkalan Nijeriya, Mai shari’a Olukayode Ariwoola ya rantsar da shi a matsayin shugaban kasan Nijeriya.
Akwai akalla nade-naden mukamai guda uku da ya kamata sabon shugaban kasa ya yi nan take, domin ci gaba da tafiyar da harkokin gwamnatisa, yayin da sauran mukaman da za su biyu baya dole ne sai majalisa ta amince da su.
Mukaman guda uku sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, shugaban ma’aikata da kuma mai magana da yawun shugaban kasa.
An dai yi ta ce-ce-kuce kan nade-naden mukamai a kan gwamnatin Tinubu da suka hada da na ministoci tun bayan da zababben shugaban kasar ya lashe zabe a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ana sa ran wasu makusantan Tinubu ne za su samu manyan mukamai a cikin gwamnatinsa, wanda wasu ke ganin cewa ya kamata ya bi cancanta da kwarewa ba la’akari da kusance ba.
Wata majiya da ke kusa da zababben shugaban kasa ta bayyana cewa makusantansa da abokai ne za su mamaye majalisar zartarwarsa.
Tinubu bai fito fili ya bayyana jerin sunayen wadanda zai nada mukamai ba a kowane mataki, walau masu taimaka masa da jami’an fadar shugaban kasa da kuma ministoci.
Masu kamun kafa na neman mukamai a sabuwar gwamnatin Tinubu sun fara kunfar baki tun lokacin da ya fara bayar da mukami a gwamnatinsa.
Shugaban kasa Tinubu ya nada Dele Alake a matsayin mai magana da yawunsa, sa’o’i kadan bayan rantsar da shi.
Alake ya dade tare da Tinubu, inda har ya taba rike mukamin kwamishinan yada labarai da dabaru a karkashin Tinubu da ga 1999 zuwa 2007 a lokacin yana gwamnan Jihar Legas.
Haka kuma shugaban ya nada, Ambasada Kunle Adeleke a matsayin zagin shugaban kasa.
Ya kuma nada shugaban matasan APC na kasa, Olusegun Dada a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen yada labarai na zamani.
Mukaman sun fara aiki nan take.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda ake sa ran za su samu manayan mukamai dai sun hada da tsohon shugaban majalisar wakilai, Mista Femi Gbajabiamila da tsohon ministan ayyuka da gidaje, Mista Babatunde Fashola da kuma tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai da Mista James Faleke.
Masana harkokin mulki na ganin cewa tun daga lokacin da sabon shugaban kasa ya fara nada mukamai ake gane kamun dudayin mulkinsa. Sun ce idan ya nada mutanen kwarai, to gwamnatinsa za ta iya samun nasara, idan kuma ya nada akasin haka, to gwamnatinsa babu abin da za ta iya tabukawa.