Asabar din nan ne, aka fara bikin mika wutar gasar wasannin jami’o’in duniya (FISU) karo na 31, wadda za a fara nan da kwanaki 48 a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang ne ya kunna wutar a wani biki da aka gudanar a harabar jami’ar Peking, ya kuma sanar da fara mika wutar gasar.
Mukaddashin shugaban gasar ta FISU Leonz Eder ya bayyana a wani sakon bidiyo da ya aike a wurin bikin cewa, mika wutar zai isar da ruhi da yanayin gasar wasannin FISU ga duniya baki daya.
Ya bayyana cewa, wakilai matasa daga kasashe da yankuna da dama, za su isar da sako mai karfi na “aiki tare don samar da makoma mai haske ga daukacin bil-adama”, a matsayin masu dauke da wutar gasar wasannin FISU ta Chengdu 2021. (Mai fassarawa: Ibrahim)