A jiya Lahadi 17 ga watan nan ne aka fara watsa shirin talabijin, na zababbun kalaman da shugaba Xi Jinping ya fi kauna a kasar Brazil. Shirin wanda kafar CMG ta kasar Sin ta tsara, aka kuma dauka da harsuna daban daban, na kunshe da tsoffin kalaman gargajiya na kasar Sin, wadanda shugaba Xi ke amfani da su a cikin jawabai da makalolinsa.
An fara watsa shirin na harshen Portuguese ne a gabar da shugaban na Sin ya isa kasar Brazil, don halartar taron kolin kungiyar G20 karo na 19, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar Brazil.
Zango na 3 na shirin ya mayar da hankali ne ga jigon yayata al’adun gargajiya da aka gada, da wayewar kai a fannin kare muhallin halittu, da musaya da koyi da juna. Kazalika, ya tattaro jawabai na ainihi, da wasu kalamai masu daraja na gargajiyar kasar Sin, wadanda shugaba Xi ke amfani da su wajen fayyace labarai, da hikimomin kasar Sin, tare da basirarsa ta musamman ta fuskar siyasa, da ma gogewarsa ta fuskar sanin tarihi da ilimin al’adu. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)