Jiya Asabar 12 ga watan nan, aka fara zirga-zirgar ababen hawa a kan babbar gada ta Cocody da kamfanin gine-gine na kasar Sin mai suna CRBC ya gina, a Abidjan, babban birnin kasuwancin kasar Kwadibwa.
Wasu manyan jami’an Kwadibwa da Sin, sun halarci bikin kaddamar da gadar, ciki har da shugaban Kwadibwa, Alassane Dramane Ouattara, da ministan kula da na’urori da kyautata hanyoyi na kasar, Amedé Koffi Kouakou, da jakadan Sin dake Kwadibwa Wu Jie.
A jawabin sa yayin bikin, shugaba Alassane Ouattara ya gode wa gudummawar da kamfanin na kasar Sin ya bayar, a fannin gina wannan babbar gada, yana mai cewa, gadar za ta yi amfani sosai wajen saukaka matsalar cunkoson ababen hawa a cikin birnin Abidjan, kuma aikin zai taka rawa wajen inganta kyautata rayuwar dan Adam, kana abun alfahari ne ga jama’ar kasar.
A nasa bangaren, Amedé Koffi Kouakou, cewa ya yi gadar Cocody muhimmiyar alama ce a birnin Abidjan, wadda ta samar da guraben ayyukan yi kimanin 3000 ga jama’ar birnin. (Murtala Zhang)