Mahdi M Muhammad" />

An Ga Cajar Waya A Mafitsarar Wani Mutum Yayin Tiyata

Likitoci a wani asibiti a Indiya sun shiga cikin damuwa bayan cire kebul da suka yi na wayar hannu wanda ya kai kusan kafa 2 daga mafitsarar wani saurayi dan shekara 30 bayan sun yi masa aiki a cikinsa da farko.

Mara lafiyar ya fadawa likitocin cewa ya hadiye kebul din ne ta bakinsa, amma likitocin sun gano cewa kebul din ya shiga cikin mafitsarsa ne ta cikin azzakari. Daga nan likitocin suka yanke shawarar yin gwajin ‘stool’ da ‘endoscopy’ don sanin inda wayar take.
“Mun yi binciken kwakwaf akan wannan lamari amma ba mu ga wayar ba. Lokacin da muka yi masa aiki, babu wani abu a bangaren hanji,” kamar yadda Dakta Walliul Islam dan asalin Guwahati ya shaida wa Timesnownews.
Hanya guda daya da za a gano hakikanin dalili shi ne dauki hoton ‘d-Ray’ kafin mutumin ya shiga tiyata. Ba zato ba tsammani, sakamakon da hoton ya nuna ya ba wa likitan da tawagarsa mamaki, a inda aka bayyana cewa kebul din yana cikin mafitsarar mara lafiyar ne.
Likitan ya ce, “Ya gaya mana cewa ya hadiye wayar ne ta bakinsa, amma a zahiri ya saka abun ne ta hanyar azzakarinsa. Na kwashe shekaru 25 ina gudanar da aikin tiyata amma wannan shi ne karo na farko da na fara ganin irin wannan lamarin.”
Ya kara da cewa, mutumin yana da dabi’ar sanya abubuwa a cikin cikinsa ba wai kawai waya ba, har ma da wasu abubuwa. Ya ce, “ya yi hakan ne don ya samun damar gamsar da kansa ta hanyar jima’i. Wani nau’in gamsar da kai ne da ake kira ‘urethral sounding’, wanda shi ne sanya abu ko ruwa a cikin al’aurarka”.
Bugu da kari, wannan hanyar gamsar da kan ba sabon abu bane, domin maza sukan yi hakan a wasu lokuta. Amma wannan mutumin ya wuce gona da iri saboda ya bar kebul din ya isa mafitsararsa ta fitsari, “in ji Islam”.
Ya ci gaba da cewa, mutumin ya zo wurin likitocin kwana biyar bayan faruwar lamarin, kuma ya ci gaba da musanta cewa ya hadiye kebul dinne ta bakinsa. Kuma da ya fadi gaskiya da abin ba zai kai ga tiyata ba. Ya yi hakan ne kawai don jin dadin jima’i, kuma babu wani abin da ke damun shi. An cire kebul din kuma mara lafiyar yana samun sauki sosai.

Exit mobile version