Rahotanni sun bayyana cewa, farashin Soya ya fadi kasa war was a wasu kasuwannin da ke a jihar Neja, biyo bayan da manoman na Doyar a jihar suka fara cika kasuwannin jihar da Doyar.
Bisa binciken da aka gudanar a manyan kasuwannin da ke a jihar, musamman a kasuwar sa ke a shalkwatar Paiko da ke a cikin karamar hukumar Paikoro da kuma wanda aka gudanar a kasuwanin Gwari da Gwadabe da ke a garin Minna a cikin jihar ta Neja sun nuna cewa, farashin na Doyar ya fadi kasa war was da kusan kashi 30 a cikin dari.
Daya daga cikin masu sayar da ita a kasuwar Paiko Mohammed Salihu, ya sanar da cewa, Doya kwarya 100 da ake sayar wa akan farashin naira 200,000 a baya, a yanzu ana sayar da ita daga naira 40,000 zuwa naira 70,000, inda ya ce, amma ya danganta da girman da Doyar yake da shi.
Mohammed ya ci gaba da cewa, sai dai, har yanzu akwai manomanta da ba su fara kawo ta su Doyar da suka noma zuwa kasuwanni ba, ganin cewa, a yanzu suna ci gaba da more garabasar girbin Waken Soya da suka noma a kakar noman bana ba domin suna da burin masu saye da za su sayar wa da amfanin akan sabon farashi idan farashin ta ya tashi a daga cikin watan janairun, inda hakan zai kasance dai dai da lokacin da suke shirye-shiyen sake sabon yin shukar ta.
Wasu manoman Doyar musamman wadanda suke a yankunan, Munya, Paikoro, Shiroro, Rafi da kuma na sauran wasu kananan hukumomin da ke a cikin jihar sun bayyana cewa, duk da rashin tsaron da suke fuskanta a yankunan na su, sun samu nasarar yin girbi mai yawan gaske a kakar noman ta bana.
A wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa, wasu manoma da suka tashi daga yankunan Shiroro, Munya, Rafi da Paikoro a lokacin daminar da tawuce saboda kalubalen rashin tsaro a yankunan, zuwa wasu yankunan da ba fuskantar kalubalen na rashin tsaron hakan ya ba su sukunin nomanta da dama, inda hakan ya sa suka samu yin girbi mai yawan gaske.
Shi ma wani mai sayen Doyar a kasuwar Gwadabe da ke a garin Minna Mohammed Musa ya tabbatar da faduwar farashin na Doyar, inda ya ce, a yanzu ya sayi Doyar babba akan naira 3,500, wacce a baya, ya sayi daga naira ar 8,000 zuwa naira 9,000.
Liman Mohammed, wani mai sayen Doyar ya ce, ya sayi Doyar kwaya takwas a ‘yan makwanin da suka shege daga naira 6,000 zuwa naira 12,000, amma a yanzu farashin ta sauka kasa matuka.
Wani mai sayen Doyar Abubakar Yahaya ya bayyana cewa, a yanzu ya sayi duk babbar Doyar duk kwaya daya a farashi daga naira 1,500 zuwa naira 2,000 wacce a baya ake sayar da duk kwaya daya babba daga farashin naira 3,000 zuwa naira 5,000.
Shi kuwa Yakubu Mustapha ya ce, farashin na Doyar ya karye ne saboda sabuwar ta da aka cike kasuwanin da ita.