CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

An Gano Kwayar Cutar Corona A Cikin Ruwan Masai A Watan Nuwamban Bara A Brazil

by CRI Hausa
July 4, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
1 min read
An Gano Kwayar Cutar Corona A Cikin Ruwan Masai A Watan Nuwamban Bara A Brazil
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wata tawagar masu bincike daga jami’ar tarayya ta Santa Catarina ta Brazil, ta sanar da cewa, an samu wasu birbishin kwayoyin cutar Corona a ruwan masai, a watan Nuwamban bara a Florianopolis, babban birnin jihar Santa Catarina ta kasar.

Daga ranar 30 ga watan Oktoba, zuwa 4 ga watan Maris, tawagar masu binciken ta tattaro samfuran ruwan masai na wurare daban daban guda 6, a biranen Florianopolis da Santa Catalina.
Binciken nasu ya zo ne watanni 2 kafin a samu bullar na farko a hukumance a nahiyar Amurka a ranar 21 ga watan Junairu, haka kuma kafin samun bullar cutar a kasar, a karshen watan Fabreru.
Rahoto da tawagar masu binciken 14 ta fitar, ya ce sun gano kwayar cutar Corona a samfura 2 da suka samo a ranar 27 ga watan Nuwanban 2019, tun kafin a samu bullar cutar na farko a nahiyar Amurka.
Sun ce sakamakonsu ya nuna cewa, kwayar cutar ta yi ta bazuwa a Brazil tun cikin watan Nuwamban 2019, tun kafin samu bullarta a nahiya Amurka.
Baya ga Brazil, an gano kwayar cutar a ruwan masai a kasashen Spaniya da Italiya a bara tun kafin a samu bullar cutar na farko a Turai a farkon bana. (Fa’iza Mustapha)

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Ko Wasu ’Yan Siyasar Austriliya Sun Zama Mahaukata Wajen Adawa Da Kasar Sin Sakamakon Rudanin Tunaninsu

Next Post

Pantami Ya Karyata Zargin Siyan Gidaje Uku A Abuja

RelatedPosts

Allurar Rigakafin Da Sin Ta Samar Na Da Inganci

Allurar Rigakafin Da Sin Ta Samar Na Da Inganci

by CRI Hausa
51 mins ago
0

Ran 30 ga watan Disamba na shekarar bara, bayan allurar...

Rikicin Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Ya Jawo Asarar Guraben Ayyuka 245,000 A Amurka

Rikicin Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Ya Jawo Asarar Guraben Ayyuka 245,000 A Amurka

by CRI Hausa
5 hours ago
0

Wani nazari da cibiyar binciken harkokin tattalin arziki ta Oxford...

Amurka Za Ta Yi Wa Kanta Illa, Idan Ta Ci Gaba Da Hana Hajojin Jihar Xinjiang Shiga Kasar

Amurka Za Ta Yi Wa Kanta Illa, Idan Ta Ci Gaba Da Hana Hajojin Jihar Xinjiang Shiga Kasar

by CRI Hausa
5 hours ago
0

kwanan nan, hukumar kwastan da hukumar kare iyakokin Amurka, sun...

Next Post
Tattalin Arzikin Nijeriya

Pantami Ya Karyata Zargin Siyan Gidaje Uku A Abuja

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version