Wani sabon bincike ya nuna cewa mutanen da ke yawan barbada gishiri a kan abincinsu musamman wanda aka dafa na fuskanatar barazanar mutuwa da wuri.
Binciken, wanda aka wallafa a mujjalar European Heart da kuma ya kunshi mutane kusan rabin miliyan, ya gano cewar mutanen da ke kara gishiri a abincinsu, suna kara wa kansu kashi 28 na yiwuwar mutuwa da wuri.
- Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Binciki Buhari Da Gwamnatocin Baya Ba – Peter Obi
- ‘Yan Nijeriya Na Da Riko Da Addini, Amma Hakan Bai Hana Su Sata Da Zamba Ba – Buhari
Sannan, binciken ya bayyana cewa maza da suka kai shekara 50, na rage wa kansu lokacin rayuwa a duniya ta hanyar kara gishiri a abincin.
Farfesa Lu Qi, wanda ya jagoranci binciken a kasar Amurka, ya ce ko da rage yawan shan gishiri ma, na iya haifar da fa’ida mai yawa ga lafiyar jikin mutum.
Masana binciken lafiya sun bayyana yadda yawan cin gishiri ke da matsala ga lafiyar mutum, musamman ga wadanda shekarunsu suka ja.