An bayyana sunayen wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su daga Dogon Noma a unguwar Unguwan Gamo da ke karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa an yi garkuwa da wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba a ranar Asabar 16/3/2024 da misalin karfe 6:00 na safe lokacin da ‘yan bindiga da dama suka mamaye yankin.
- Sojoji Sun Kashe Mahara 14, Sun Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna Da Neja
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 9, Sun Yi Garkuwa Da 20 A Kaduna
Tsohon shugaban karamar hukumar Kauru, Hon. A baya Cafra Caino, ya tabbatar da kai harin sai dai ya kasa tantance adadin mutanen da aka yi garkuwa da su a ranar.
Sai dai a yanzu Caino ya tabbatar da cewa an yi garkuwa ne da mutane 14 da suka hada da maza uku da mata 11 sannan kuma mutum daya ya samu rauni yayin harin.
Sunayen wadanda aka yi garkuwa da sun hada da;
1. Bulus Dandaura
2. Murna Bulus
3. Donald Bulus
4. Labari Audu
5. Zainabu Dauda
6. Dorcas Titus
7. Jummai Garba
8. Felicia Wanzami
9. Ruth Thomas
10. Esther Oliver
11. Comfort Babangida
12. Mrs Yakubu Pama, 13. Abaza Monday
14. Christy Samuel
Sai dai Jibrin Dauda ya samu munanan raunuka wanda ya kai ga mika shi asibiti domin kula da lafiyarsa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, bai tabbatar da kai harin ba, saboda an kasa samun lambar wayarsa har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Kazalika, gwamnatin jihar Kaduna ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan sabon harin da aka kai a jihar ta Kaduna.