Mutane da yawa da suke tunanin hutu zuwa Afirka suna yin shiri domin zuwa kasar Maroko a zuciyarsu, ko kasar Afirka ta Kudu a wasu lokuta, watakila wasu su yi tunanin zuwa irin su Kenya, da Masar don ganin shahararrun abubuwan tarihi da suka hada da Dala wato (pyramids), ko kuma kogin Nil mai tsayin mil 4,100 wanda hakan na samar da wayewar kai.
Amma duk da haka, a matsayinta na nahiya, Afirka tana da kasashe 54, kusan adadin jihohin Amurka.
Ko da yake yana iya zama abin mamaki, kusan dukkanin wadannan kasashe suna da aminci kuma suna da abubuwa na jin dadi iri daya kamar wadanda aka samu a yawancin kasashen duniya na farko.
Alal misali, dauki Aljeriya, kasa mafi girma a Afirka fiye da girman Tedas sau uku. Wannan kasa ta Arewacin Afirka tana da Dala kamar Masar, da tarkace masu ban sha’awa da yawa wadanda za su yi sha’awar duk wani mai son tarihi.
Rahotanni daga Kasar Algeria na cewa kasar za ta gina katafaren masallacin da ba irin sa a duniya a wajen girma, domin ya zame wa kungiyoyin Musulmi masu matsakainci ra’ayi wani babban kalubale.
Kanfanin Dillacin labarai na Kasar Faransa AFP ta ruwaito cewa masallacin na Djamaa El Djazir za a gina shi ne a tsakanin wani yanki dake tasowa a fannin yawon bude ido da wata tsohuwa gunduma da a can da take zaman matattarar kungiyoyin ‘yan tsageran addini.
Mai Bai Wa Ministan Harkokin Gida Shawara,Ahmed Madani wanda shi ne ke da alhakin gina masallacin, ya shaida wa APF cewa da farko wasu sun soki lamirin su cewa gwamnati na gina wa wasu masu ra’ayin rikau wurin ibada ne, amma a kashin gaskiya hukuma na gina wannan masasllacin ne don ya zama babban kalubale ga irin wadanan kungiyoyin.
An dai kiyasta cewa masallacin zai lakume kudi har Dalar Amurka milyan dubu da milyan 400, kuma abubuwan da za a samar cikin sa za su hada da dakin karatu da zai iya daukar littafai har miliyan guda, da makarantar Al’kurani, da dakin adana kayan tarihi, da kuma Hasumiya mafi tsawo a duniya mai tsawon mita 265, da kuma farfajiyar masallacin da za ta iya kwashe mutane dubu 120 a lokaci guda.
Madani ya ce anasa ran a kammala ginin wannan masallacin cikin shekara mai zuwa. Mun ciro muku daga BOA