An gudanar da taron manyan jami’ai karo na 16, na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC a birnin Beijing, fadar mulkin ksar Sin. Yayin taron na jiya Litinin, an nazarci rahoton kasar Sin game da aiwatar da sakamakon taron ministoci na 8, na kasashe mambobin dandalin, tare da musayar ra’ayoyi game da shirin gudanar da sabon taron shekarar dandalin na 2024 dake tafe.
Cikin jawabin da ya gabatar yayin taron, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Deng Li, ya ce Sin a shirye take ta hada gwiwa, da amincewar juna tsakaninta da nahiyar Afirka, tana kuma fatan wanzar da zaman lafiya da daidaito, da musaya, da koyi da juna tsakaninta da sauran sassan wayewar kai, kana ta shirya tunkarar taron na FOCAC na shekarar badi.
- Gwamnatin Tarayya Ta Karbi ‘Yan Nijeriya 108 Da Suka Makale A Nijar
- Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina Za Ta Fara Bai Wa Malamai Da Masu Unguwanni Alawus
Deng Li ya ce, ta hanyar aiwatar da matakan yin aiki tare kan turbar zamanintarwa, Sin da kasashen Afirka, za su bude sabon babin samar da ci gaba, da inganta kai tsakanin kasashe masu tasowa.
A sasa bangare kuwa, babban mashawarcin shugaban kasar Senegal kan harkokin waje, kuma jagoran hadin gwiwa na taron Oumar Demba Ba, cewa ya yi tun kafuwar dandalin FOCAC, kasashen Afirka da Sin sun ci gaba da bunkasa hadin gwiwarsu bisa abota, da martaba juna, da amincewar juna, da kuma cin moriya tare.
Demba Ba ya kuma godewa kasar Sin bisa yadda ta aiwatar da tarin ayyukan more rayuwa a sassan kasashen Afirka, ta kuma nunawa duniya aniyar samar da gajiya bisa hadin gwiwa, wanda hakan ya haifar da dunkulewa, da daidaito, da managarcin tsarin hadin gwiwa, wanda ke tabbatar da bunkasuwa a nan gaba.
Daga nan sai jami’in ya godewa yadda Sin din ta goyi bayan shigar kungiyar AU cikin kungiyar G20, da irin kyakkyawar rawar da ta taka wajen inganta wakilcin kasashe masu tasowa, da ingiza sauye-sauye a tsarin gudanarwa na kasa da kasa bisa adalci da sanin ya kamata.
Taron na jiya Litinin dai ya hallara kusan manyan baki 300, da jami’ai da wakilai daga Sin, da na kasashen Afirka 53, da mambobin hukumar zartaswar kungiyar AU, da sauran dandaloli, baya ga masu sa ido daga wasu hukumomin kasa da kasa da na shiyyoyi. (Saminu Alhassan)