An gudanar da zanga-zanga a Jos da ke jihar Filato a ranar Laraba domin martani ga hukuncin da kotun daukaka kara da ta yanke na korar mambobin jam’iyyar PDP daga majalisar dokokin kasar nan.
Masu zanga-zangar wadanda galibinsu matasa ne maza da mata, sun nuna rashin jin dadinsu game da hukuncin kotun daukaka kara da ya soke nasarar zaben da ‘yan takarar PDP suka samu a majalisar dattawa da ta wakilai.
- Wadanne Damammaki Da Aka Samu Cikin Abubuwan Da Aka Nuna A Karon Farko A Duniya A CIIE?
- Burin Sin Na Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya Bai Sauya Ba
Masu zanga-zangar dai na dauke da alluna daban-daban domin nuna damuwarsu da rashin amincewa da zabin doka ta yi watsi da zabin da suka yi a rumfunan zabe.
Da yake jawabi ga masu zanga-zangar a unguwar Maraba Junction Roundabout, karkashin inuwar masu ruwa da tsaki a Filato, Wakili Ibrahim Yakubu, ya bukaci majalisar shari’a ta kasa da ta duba hukuncin kotun daukaka kara.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta soke zabukan da aka yi na dukkan ‘yan majalisar PDP na manya da kananan hukumomi saboda rashin mutunta umarnin kotu na shirya zabukan kananan hukumomi da na majalisun jihohi na jam’iyyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp