Rundunar ‘yansandan a Jihar Legas ta gurfanar da wani malami mai suna Omobolanle Micheal Olaniyi mai shekaru 25 a gaban kotun laifuffukan jima’i bisa cin zarafi a Ikeja, karkashin jagorancin mai shari’a Ramon Oshodi, bisa zargin yin lalata da wata daliba ‘yar shekara shida.
PUNCH Metro ta tattaro cewa wanda ake zargin wanda aka kama a ranar 24 ga watan Yuli, 2023, ana tuhumar sa ne da laifin cin zarafin wata yarinya da kuma lalata ta hanyar jima’i da ita.
- An Kama Wasu Ƴansanda Kan Zargin Kisan Ɗalibin Jami’ar Kwara
- Kingibe Ya Yaba Wa Tsare-tsaren Bunkasa Ilimi Ga Matasa Na Buratai
A cewar lauyan mai shigar da kara, B. E. Okeowo, laifukan sun saba wa sashe na 135 da 261 na dokokin laifuka na Jihar Legas, na shekarar 2015.
PUNCH Metro ta samu labarin cewa laifin ya faru ne a makarantar Oliber Care Montessori Ogba inda Olaniyi malami ne, ita kuma daliba ce wacce abin ya shafa.
A cewar tuhume-tuhumen, Olaniyi ya taba cinyar wacca abin ya shafa da rashin kunya, sannan ya dauke ta kuma ya lalata da ita ta hanyar shigar da yatsunsa a cikin farjinta.
Sai dai wanda ake tuhumar ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Ramon Oshodi ya bayar da umarnin a tsare wanda ake zargin a gidan yari sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Fabrairun 2025 domin ci gaba da shari’ar.