Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya, Abuja ta ce ta gano ba gaskiya ba ne rahoton da wasu mazauna yankin 14 suka yi cewa an sace musu mazakuta ba.
Kwamishinan ‘yansandan babban birnin tarayya, Haruna Garba, ya ce an gano rahoton ba gaskiya ba ne, bayan da aka duba lafiyar wadanda abun ya shafa.
- Libya Ta Ba Da Umarnin Tsare Jakadiyar Brussels Kan Zargin Cin Hanci Da Rashawa
- Jami’ar Danfodiyo Ta Musanta Harin ‘Yan Bindiga A Harabar Jami’ar
Garba ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja kan nasarorin da rundunar ta samu a yaki da miyagun laifuka.
Ya kara da cewa mutane 14 da ke da hannu a lamarin a halin yanzu ana ci gaba da bincike a kansu bayan an tabbatar da karyar da suka yi.
“Ana tuhumar su da bayar da bayanan karya da kuma tayar da hankalin jama’a.
“Sun yaudari ‘yansanda wajen tunkarar wani harin da aka kai kan sama da mutane 10 da ake zargi a birnin tarayya a cikin ‘yan makonnin da suka gabata.”
Garba ya ce an sanar da ‘yansandan rahotanni sama da 10, galibinsu a kewayen Garshi, Gwagwalada da Kwali da ke cikin babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce wasu daga cikin wadannan rahotanni ba su da tushe.
Sai dai shugaban ‘yansandan ya ce ba a samu asarar rai ba a lamarin ba.
“Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja ta tattara rahotanni sama da 10 da ake zargi da bacewar mazakutar maza a fadin yankin da kuma kara ta’azzara rikicin da matasa masu fusata ke yi.
“Rundunar ‘yansanda ta dauki matakin hana asarar rayuka da dukiyoyi da kuma dawo da doka da oda.
“Mutane 14 da ake zargi da cewa bacewar mazakutar tasu, an kai su asibiti inda likitan ya tabbatar da cewa sassan jikin nasu yana kuma suna aiki.
“Saboda haka, an gurfanar da su gaban kotu da laifin bayar da bayanan karya da kuma tayar da hankalin jama’a,” in ji shi.
Garba ya yi kira ga mazauna yankin da su gargadi ‘ya’yansu da su daina tayar da hankulan jama’a.