Daga Idris Aliyu Daudawa,
Ranar Laraba ce aka gurfanar da mtane biyu Nicolas Asindu, 43 da Jacob Mashi, a gaban kotun majistare ta Ikeja Legass, inda ake tuhumar su da aikata zamba cikin aminci.Ana dai tuhumar su da samun kudaden da suka kai Naira milyan daya da rabi (1.5 ) da niyyar bayar da haya giuda mai daki biyu na kwana.Asindu, mai shekaru 43, dan kasuwa ne da Mashi, 26, dukkansu masu gadi ne, suna kuma zaune ne a Ikeja, an same su da aikata laifuka uku, wadanda suka hada da hada kai, samun kudade ta hanyar karya, da kuma sata.
Amma basu yarda da sun aikata lafi ba.Mai gabatar da masu laifi mataimakin safurudenda na dansanda (ASP ) Ezekiel Ayorinde, ya bayyanawa kotu cewar mutanen biyu sun aikata laifukan ne ranar 14 ga watan Oktoba 2020 a, Opebi, Legas.Ayorinde ya ce wadanda suka aikata laifin da gangan ne suka samu kudaden, ne daga wurin Sandra Nnamadi da Cynthia Nnamadi, da niyyar samar masu gidan haya, ba layi mai namba sha shida. , Aderoju Adewuyi Ikeja.Bayan da masu shigar da karar suka biya kudin kuma suka kawo kayansu sai mai gidan ya musanta cewar ya san wadanda ake karar.
“Kokarin da masu amsar gidan haya suka yi suka yi na karbo kudadensu daga wadanda ake tuhumar, abin ya ci tura domin ba a same su ba kuma sun ki zuwa lokacin da aka neme su. “Daga baya aka cafke su aka kai su ofishin,’ in ji mai gabatar da kara. Ayorinde ya bayyana cewar laifukan sun sabawa sassa na 287, 314 da kuma 411 na dokar manyan laifuka ta jihar Legas, 2015.