Ofishin ‘yansanda da ke a Tundun Wada a Karamar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna, ya gurfanar da tsohon Alkalin Kotun Majistari Khadi Muhmmud Shehu, bisa zargin kutsawa cikin gidan wata matar aure, mai suna Sadiya Muhmmad Halliru tare da lakada mata duka.
Tun da farko, an gurfanar da wanda ake zargin ne, a ranar Talatar da ta gabata a gaban kotun Majistari da ke a Zariya.
- Kwalara: Kwara Ta Rufe Gine-gine 14 Saboda Rashin Banɗaki, Ta Gargaɗi Masu Gidaje
- Ambaliyar Ruwa Ta Katse Hanyar Maiduguri Zuwa Damboa
Dansanda mai gabatar da kara Sufeta Adamu Abubakar ya shaida wa kotu a yayin da ya gabatar da karar wanda ake zargin cewa, laifin da ake zargin tsohon alkalin, ya saba wa sashi na 327 da na 237 da kuma 239 na kudin Final Kod da aka samar a 2017 a Jihar Kaduna.
Ya kara da cewa, tun da farko mijin matar mai suna Garba Adda’u da ke zaune a unguwar Ginar Ganye da ke a cikin Tudun Jukun Zariya ne, ya shigar korafi a kan zargin a caji ofis din ‘yansanda da ke a Tundun Wada rarar 6 na watan Satumbar 2024.
Ya shaida wa kotun cewa, mijin matar ya zargi tsohon alkalin kan shigar masa gida tare da rufe daki da matar ya kuma lakada mata duka ciki har da dukan wasu kannenta biyu, wanda hakan ya sa ta samu raunuka kuma aka kai ta asibiti na matakin farko, don a yi mata magani.
Sai dai, tsohon alkalin a gaban kotun, ya karyata wannan zargin da ake yi masa.
Lauya mai tsayawa alkalin S.M Abubakar ya roki kotun da ta bayar da belin wanda ake zargin.
Amma dansanda mai gabatar da karar, ya bukaci kotun kar ta bayar da belin, inda ya kafa hujjarsa da cewa, mai karar da wanda ake karar, makotan juna ne, kuma bayar da belinsa, zai iya jefa rayuwar mai karar a cikin hatsarin barazana.
Da yake gatabatar da bayani, babban alkalin Kotunn Majistarin Lukuman Sidi, ya bayar da belin tsohon alkalin a kan Naira 50,000 tare da kawo mutum daya da zai tsaya masa, wanda kuma ya mallaki fasfo na kasa da kasa kuma mazauni a yankin da kotun take da zamanta.
Kazalika alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Okutobar 2024.