Daga Bello Hamza,
A gurfanar da wani mai suna Monsurat Obafemi mai shekara 47 a duniya kuma ’yar kasuwa a bisa laifin zamba cikin aminci inda ta karba N60,000 ta hanyar yaudara.
Obafemi, wadda ke zaune a unguwar Alagbado a jihar Ogun, na fuskanta tuhumar karbar kudaden ne ta hanyar yaudara da kuma sata.
Dan sanda mai gabatar da kara, Sgt. Olasunkanmi Adejumola, ya bayyana wa kotun cewa, wanda bake zargin ta aikata laifin ne a watan Agusta na shekarar 2020, a unguwar Ogba, ta jihar Legas.
Ya kuma ce, laifin ya saba wa sashi na 287 da 315 na dokokin manyan laifukka na jihar Legas na shekarar 2015.
Daga nan ne alkaliyar kotun, Mrs O. A. Odubayo, ta bayar da belin wadda ake zargin akan kudi N20,000 ta kuma daga karar zuwa ranar 18 ga watan Janairu 2021 don cigaba da sauraron shari’ar.