Ranar Litinin din da ta gabata ne, Malam Ismail Bello, ya maka Hafsat Auwal a gaban wata kotun Shari’ar Musulinci da ke Kaduna, bisa zargin yin garkuwa da matarsa da kuma jaririn da aka Haifa masa bayan kwana daya. Bello, ya gayawa kotu cewa, Auwal, wanda yake dan’uwan matarsa ne, ya zo gidansa da wata mata, wadda ta sace matarsa da kuma dansa, wanda aka Haifa masa a ranar.
Saboda haka, sai ya bukaci kotu, ta matsa mata ta dawo da matar da kuma wannan jariri. Sannan kuma Bellon ya roki kotu ta tursasa musu su biya shi kudi, saboda tashin hankalin da suka jefa shi a ciki.
Auwal, ya gayawa kotu cewa, sun dauki matar sun kai ta gidan iyayenta,bayan ta haihu kamar yadda suka bukaci matar ta kula da kayanta na dan wani lokaci kafin ta dawo.
Mai shari’a, Malam Salisu Abubakar Tureta, ya ce, ba zai ci gaba da sauraren karar ba, saboda matsala ce wadda ta kamata a warware ta a cikin gida.