Rahotanni daga Jihar Kano sun tabbatar da cewa an harbe wani tsohon kansila bisa zarginsa da sace akwatin zabe.
Lamarin ya faru ne a yayin da ake gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majaliasar dokokin jiha a ranar Asabar.
- Zaben Gwamna: Kwamishina Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Hannun ‘Yan Daba A Zamfara
- Matashin HK Ya Bayyana Kwarin Gwiwa Kan Kwanciyar Hankalin Yankin A Taron MDD
Rahotannin sun ce sojoji ne suka harbe Ibrahim Nakuzama, wanda tsohon kansila ne a mazabar Getso da ke Karamar Hukumar Gwarzo.
Sai dai kawo yanzu Rundunar Sojin Nijeriya ba ta kai ga fitar da sanarwa kan lamarin ba.
Wani makusancin mamacin ya ce tuni aka yi jana’izarsa a mahaifarsa a Getso.
Makusancin, ya ce suna cikin jimamin rashin Ibrahim din, don haka babu wani bayani da zai kara.
Ibrahim Nakuzama ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya shida.
Jihar Kano dai an samu yamutsi a wurare da dama a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar.
Sai dai jami’an tsaro sun lashi takobin saka kafar wando daya da duk wanda ya shiga hannu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp