Ana fargabar mutane da dama sun mutu, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata, sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin ‘yan daba da jami’an tsaro a Jihar Kano.
Yankunan da lamarin ya shafa sun hada da Rijiyar Lemo, Kurna zuwa Bachirawa a karamar hukumar Fagge, Kofar Nassarawa a karamar hukumar Birni, da Unguwa Uku a karamar hukumar Tarauni.
- Tinubu Zai Yi Wa ‘Yan Nijeriya Jawabi A Ranar Lahadi
- Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
A cewar wasu shaidun gani da ido, arangamar ta fara ne a lokacin da wasu matasa suka bijirewa dokar hana fita da aka sanya a jihar tare da fitowa kan tituna, inda suka ci gaba da zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali a Kano.
Wani mazaunin Rijiyar Lemo mai suna Abdulkadir Musa ya ce, “Akalla mutane takwas ne aka harbe a yankinmu da suka hada da mata da yara. Yanzu haka wata tsohuwa ta mutu tare da wasu uku, yayin da da dama suka samu munanan raunuka.
“A gaskiya abin da ya faru shi ne, kun san har yanzu dokar hana fita tana nan, don haka mutane suka bijirewa hakan suka fito suna zanga-zanga. A lokacin ne jami’an tsaro suka fara kai farmaki, suna kokarin tarwatsa su, kuma ana cikin haka ne sai da suka yi harbin domin su tarwatsa masu zanga-zangar.”
Wani mazaunin garin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce ‘yan daban da suka fake da zanga-zangar yunwar, sun yi yunkurin fasa shaguna, ciki har da shagon Rufaida Yoghourt.
Ya ce jami’an tsaro sun tarwatsa ’yan daban, inda daga nan ne suka fara jifan su da duwatsu.
An bayyana cewa wani jami’in ‘yan sanda ya ji rauni a yayin arangamar, ko da yake ba a tantance shi ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Mutanen da harsashi ya rutsa da su yanzu haka suna samun kulawar likitoci a asibitin Salamatu.
Wata mai amfani da shafukan sada zumunta, Aiha K Nass, ta wallafa, “Muna nan muna makokin kakarmu; ‘yan sanda sun harbe yayana Aliyu. Yanzu haka ya mutu.”
Wani mai amfani da shafukan sada zumunta, Omar Khalid Saleh, ya rubuta cewa, “’Yan sanda a Kano sun mayar da zanga-zangar lumana zuwa wani abu daban. Me ya sa ake harbe-harbe da kashe-kashe? Kuna gayyatar matsala. Sun harbe wannan matashi ne, kuma ya mutu nan take a Kofar Nasarawa, cikin birnin Kano. #EndBadGovernance A Nijeriya #KarshenYanSanda.”
Masu zanga-zangar sun fito kan titin Zariya da ke kan Unguwa Uku amma kuma jami’an tsaro sun tarwatsa su.
An jibge karin jami’an tsaro domin dakile zirga-zirga a Kurna Asabe, kusa da Barikin Sojoji na Bukavu.
Kokarin jin ta bakin kakakin ‘yansandan jihar, ya ci tura domin har zuwa lokacin hada wannan rahoto, SP Abudullahi Haruna Kiyawa bai daga waya ba.