Hukumar Gudanarwar Birnin Tarayya Abuja (FCTA), ta hannun Sakatariyar Ci gaban Al’umma, ta kammala shirin yaye almajirai sama da 120 da su ka samu horon sana’o’i daban-daban.
Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya, Abuja, Dakta Ramatu Aliyu ce, ta bayyana hakan a wata ziyarar gani-da-ido ta yau da kullum a sakatariyar da aka saba yi, a ranar Talata a Abuja.
- Sanatocin APC Ma Su Shirin Sauya Sheka Sun Canja Tunani Bayan Ganawarsu Da Buhari
- Dubun Wadanda Suka Kwakwule Idon Wani Yaro A Bauchi Ta Cika
Almajiran dai an zaɓo su ne daga manyan titunan Abuja, inda aka yi musu gyaran hali da rayuwa a cibiyar koyar da sana’o’i ta FCT Bwari.
Ta ce horon wani bangare ne na matakan aiwatar da dabaru a wani fanni na tabbatar da alkawarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi na fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekaru 10 masu zuwa.
Ministar ta bayyana gamsuwa kan abin da ta bayyana a matsayin ‘babban sauyi’ na masu rauni a cikin al’umma.
Ta yabawa shirin da ma’aikatan gudanarwa na sakatariyar suka yi kan yadda shugaban kasa ya samar da ayyukan yi.
Sai dai ta umarce su da su kara yawan matasa a cikin shirin horaswar da nufin cimma kudirin na shugaban kasa.