An jjinjina wa Gwamna Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje bisa yaki da yake da matsalar shaye -shaye a jihar Kano. Babban mataimaki ga mataimakin shugaban majalisar Dattijai.”Senior Legislatibe Aid, LSA”. Injiniya Musa Mujahid Zaitawa shi ne ya yi wannan jinjinar da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce, a kokarin Gwamnan Kano na kawar da wannan matsala daga shugabannin zababbu ya ba da umarnin sai da aka yi gwaji akan dukkan wadanda aka tsayar takarar shugabancin kananan hukumomi 44 da Kansilolnsu gaba daya.
Injiniya Musa Mujahid Zaitawa ya ce, a kokarin samar da shugabanni na gari ga al’umna shi yasa Gwamna Ganduje ya dau wannan kyakkyawar mataki mai nagarta.
Babban mataimaki ga mataimakin shugaban majalisar Dattawan Musa Mujahid ya nemi Gwamna Ganduje ya yi aiki kafada da kafada da ofishin mataimakin shugaban majalisar dattijai ta Kasa domin yaki da wannan annoba ta shaye-shayen kwayoyi da take neman lalata rayuwar matasa maza da mata a jihar kano.
Mujahid Zaitawa ya bukaci karin hadin- kan Dokta Abdullahi Umar Ganduje akan yaki da wannan annoba ta shay-shaye domin samun nasara da kuma samun nasara ta hanyar gyaran dokar hukunta masu fataucin kwayoyin da sarafawa, dama masu shan kwayar.
Injiniya Musa Mujahid Zaitawa daga karshe ya yi fatan Allah ya baiwa Gwamna Ganduje samar cigaba da dinbin ayyuka da yake ya kuma kammala zangon mulkinsa na biyu lafiya da samun nasara akan yaki da shaye shaye ,kamar yanda yaci nasarorin akan yaki da cutar shan inna da kuma nasarori da yake dauka na lafiya daga korona ga al’umma.