A kokarin da ake na bunkasa ayyukan ‘yan jarida masu amfani da harshen Hausa a Nahiyar Afrika, an kaddamar da cibiyar kungiyar a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.
Wannan ne karo na farko da aka samar da irin wannan kungiya bisa la’akari da jajircewar da ake yi na ganin an bunkasa harsunan cikin gida musamman Hausa, wanda yake kokarin mamaye sauran harsuna a Nahiyar Afrika.
- Majalisar Wakilai Ta Gabatar Da Kudirin Kara Yawan Membobi Daga 360 Zuwa 366
- Rikicin Jam’iyyar NNPP Ya Kazanta A Kano
A yayin kaddamar da cibiyar kungiyar tare da kwarkwaryar zantawa da ‘yan jaridu na kasa da kasa, da sauran wakilai da suka zo daga sassa daban-daban ciki har da Nijeriya, masu ruwa da tsaki a wannan taro sun bayyana muhimmancin wannan kungiya wadda take da manufar aiwatar da aikin jarida nagartacce musamman zaburar da jama’a kan muhimmancin gina al’umma da samar da ci gaba mai dorewa.
Maryam Sarki Azbin, wadda ta zama jigo wajen samar da wannan kungiya, ta ce lokaci ya yi da za a rika amfani da harshen cikin gida wajen isar da muhimman sakonni ga al’umma a duk inda suke.
Sarki Azbin ta bukaci ‘yan jarida da su kauce wa abubuwan da suke bata wa aikinsu kima a idon jama’a kamar izgilanci, da maula, da kwadayi, da bambadanci da keta mutuncin masu fada a ji.
Ta kara da cewa, kungiyar ta ‘yan jarida za ta yi dukkan mai yiwa wajen zaburar da ‘yan jaridu kan yadda za su rika amfani da harshen Hausa wajen sanar da mutane abubuwan da za su amfane su a rayuwarsu ta yau da kullum.
A jawabinsa, shugaban hukumar gidan telebijin da radiyo na jamhuriyar Nijar, RTN, Abdoulaye Koulibaly ya bayyana cewa aikin jarida aiki ne da yake bukatar gaskiya da sanin makamar aiki, don haka kuskure ne ‘yan jarida suke yi wajen ba da labarai na shaci-fadi don son abin hannu wasu masu fada a ji, ko kuma nuna bangaranci yayin fitar da labarai.
Koulibali ya ce samar da wannan kungiya wata dama ce da za ta taimaka wajen magance kalubalen da ‘yan jarida suke fuskanta ta fannin gudanar da ayyukansu, musamman wajen amfani da harshe na cikin gida.
Sauran wadanda suka yi jawabi a wurin sun gamsu da tsare-tsare da manufofin da aka gina kungiyar a kan su, musamman tabbatar da hadin kai da mu’amala a tsakanin ‘yan jarida na kasashe 11 da ke Nahiyar Afrika, suna masu cewa yawan da ‘yan jaridar Hausa da ake da su a Nihiyar sun isa su taka gagarumar gudunmawa wajen magance kalubalen da ake fuskanta, da kuma karfafawa masu kwarin giwa wajen ganin sun yi abin da ya dace na kyautata rayuwar al’ummar yankin.
Shi ma a nasa bangaren, ma’aikaci a hukumar telebijin a tarayyar Nijeriya (NTA), Aliyu Rabe Aliyu ya ce, babban aikin da kungiyar ‘yan jarida masu amfani da harshen Hausa za ta sa a gaba shi ne, sauya fasalin aikin jaridar gado na ‘yan ku ci ku ba mu, ya zuwa aikin jarida na samar da mafita ga tulin kalubalen da yankin yake fuskanta ta hanyar amfani da harshen da kowa yake sonsa, kuma yake amfani da shi watau harshen Hausa.