An kaddamar da yankin gwaji na cinikayya maras shinge ko FTZ a jihar Xinjiang ta kasar Sin, yankin da shi ne irin sa na farko da Sin ta kafa a sashen iyakar arewa maso yammacin kasar.
Yayin kaddamar da yankin jiya Laraba a birnin Urumqi, shugaban gwamnatin yankin Erkin Tuniyaz, ya gabatar da lasisi uku ga yankunan da za a yi amfani da su domin hada hadar cinikayya, wadanda suka hada da Urumqi, da Horgos da kuma Kashgar. Fadin yankin na FTZ ya kai kusan sakwaya kilomita 180.
- Yaya Za A Cimma “Tsaro tare”? Dandalin Xiangshan Ya Gabatar Da Wasu Tunani
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Tauraron Dan Adam Na Tianhui-5
Kafin hakan a ranar Talata, majalissar gudanarwar kasar Sin, ta fitar da wani babban shiri game da kafuwar yankin na cinikayya maras shinge a Xinjiang, a matsayin muhimmin jigo na ingiza aiwatar da sauye sauye, da bude kofa a sabon zamani.
Yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar, mataimakiyar ministan ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin Guo Tingting, ta ce kafuwar yankin na gwaji na cinikayya maras shinge na Xinjiang, zai share fagen aiwatar da manufofin dunkule raya kirkire-kirkire na yankin, da fifikon da jihar Xinjiang ke da shi, kana zai zaburar da ci gaban hada hadar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Xinjiang, tare da bunkasa bude kofa mai nagarta, da ci gaba mai inganci, da amfanar da al’umma da harkokin kasuwanci.
Jami’ar ta kara da cewa, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, za ta mara baya ga wannan sabon yankin gwaji na cinikayya maras shinge na Xinjiang, ta yadda zai dace sosai da yanayin jihar, kana ya jawo hankali albarkatu daga abokan hulda na gida da na waje. Kaza lika za a kara azamar kyautata zuba jari, da inganta hidimomin hada hadar kudi, da ingiza ci gaban tattalin arziki ta amfani da fasahohin sadarwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)