Rundunar ‘yansandan Birnin Delhi ta kasar Indiya, ta kama wani dan Nijeriya, Patrick Ngomere, bisa zargin yin kutse a asusun imel na kamfanin Family Care Pbt. Limited, kamfanin harhada magunguna, kuma cikin zamba ya kashe Rs 11.73 lakh.
Wanda ake zargin, wanda kuma ake zargi da zama a Indiya ba tare da takardar izinin shiga ba, ana kyautata zaton yana cikin wata babbar kungiyar da ke damfarar intanet daban-daban a fadin kasar.
PUNCH Metro ta ruwaito a ranar Lahadi daga kafar yada labaran Indiya ta intanet, Millennium Post, cewa, a cewar wani rahoto da tashar bayar da rahoton laifuka ta intanet ta kasar a ranar Juma’a, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
- Yadda Wata Gada Ta Balle Ta Kashe Mutum 60 A India
- EFCC Ta Kori Ma’aikata 27 Kan Zamba da Rashin Da’a
Yin amfani da dE.com, dandamalin musayar kudi, Rs11.73 lakh (Rs1,173,000) wanda ake zargin da aka aika daga kamfanin harhada magunguna ya yi daidai da Dala 13,361
Ngomere, mazaunin Greater Noida, ya shiga tarkon ‘yansanda a kusa da na’urar ATM, bayan da aka gano wayarsa na da alaka da asusun banki na damfara.
Rahoton ya ce an fara badakalar ne a ranar 10 ga watan Disamba a lokacin da kamfanin harhada magunguna ya samu sakon imel dake nuna wani mai sayar da shi, Accent Pharma, yana neman a biya shi wani sabon asusun ajiya na banki.
Ba tare da sanin sakon imel din na yaudara ne ba, ana zargin kamfanin harhada magunguna ya aika Rs 11.76 lakh, kamar yadda PUNCH Metro ta fahimci.
Wakilinmu ya ruwaito cewa kamfanin ya gano cewa an yi kutse ne bayan an biya kudin da kuma tantancewa. Wannan ya haifar da kwakkwaran bincike daga sashin damfarar intanet na kasar.
Rahoton ya kara da cewa, “Masu bincike sun binciki email din da aka yi wa kutse zuwa Nijeriya inda suka bi diddigin kudaden a asusun bankin Manipur. Hotunan sa ido sun kai ga kama Ngomere.
“An same shi ba tare da ingantacciyar takardar biza ta Indiya ba kuma ana zarginsa da kasancewa wani babban jami’in kungiyar. An yi rajistar FIR a karkashin Bharatiya Nyaya Sanhita da Dokar Baki. Ana ci gaba da bincike.”
A watan Janairun 2025, jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa Babban Sashen Binciken Laifuka na Kuwait a Jihar Ahmadi ya kama wasu ‘yan Nijeriya biyu da laifin fashi da makami.
An kama wadanda ake zargin ne cikin sa’o’i 24 bayan sun yi fashi a ofishin musayar kudi a Mahboula, wansu gundumomi a kudancin birnin Kuwait.
Ana zargin sun saci kudaden kasashen waje da suka kai Dinar Kuwaiti 4,600, kwatankwacin Dalar Amurka kusan 14,918.69 dangane da kudin musaya na currencyconbertonline.com.