Rundunar ‘yansanda Kano ta kama shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa, bisa zarginsa da hannu wajen kashe wasu mutane uku.
Rundunar ‘yansanda sun tabbatar da kama Doguwa a ranar Laraba, inda suka bayyana cewa an kama Doguwa a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
- Nasarar Tinubu Ta Tabbatar Da Dimokuradiyya Na Raye A Nijeriya -Ganduje
- Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tinubu
Rahotanni sun bayyana cewa, ana zargin dan majalisar ne da jagorantar harin da aka kai ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a mazabarsa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane shida.
An yi zargin cewa jami’in INEC ya bayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben bayan tsare shi da bindiga.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar wa manema labarai kamun.
“Eh, mun kama Hon. Alhassan Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai dangane da zargin kisan kai. A yanzu haka yana hannunmu, kuma ana ci gaba da bincike,” in ji kakakin ‘yansandan.
Sai dai Kiyawa bai bayar da wani karin bayani kan lamarin ba, amma majiyoyi sun nuna cewa binciken ya fi karkata ne kan zargin Doguwa da hannu a harin da aka kai ofishin INEC.
Labarin kamun Doguwa dai ya jefa fargaba a fadin kasar nan, inda da dama ke kira da a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Rundunar ‘yansandan ta tabbatar wa jama’a cewa ba za su gudanar da bincike.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, mutane da yawa sun zuba ido don ganin yadda lamarin zai kasance.