Umar A Hunkuyi" />

An Kama Manoman Tabar Wiwi Da Buhuna 42 A Ogun

Jami’an rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Ogun sun kama wasu manoma guda hudu da suke zargi da kwarewa wajen noman ganyen tabar Wiwi. Inda kuma har suka kwato buhuna 42 na tabar wiwi din daga hannun su.

Wadanda ake tuhumar sun hada da, James Tiba, mai shekaru 19, Anayor Okechukwu (mai shekaru 25), John Chidi (mai shekaru 32) da Felid Tehemeh (mai shekaru 20).

Wakilinmu ya ba mu rahoton cewa an kama su ne a ranar Asabar, tare da buhunan da ake kyautata zaton na tabar ta wiwi ne guda 42, a sakamakon wani bayanin sirri da aka rada wa hedikwatar rundunar ‘yan sandan da ke Ijebu Igbo.

Kamar yanda rahoton ya nna wasu daga cikin masu noman wannan haramtacciyar tabar da suka girbe tabar na su sun bi ta wannan ganin a kwanan nan da buhunhunan tabar.

Wata sanarwa daga Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, taba cewa, a sakamkon samun rahotannin sirrin ne babban Jami’in ‘yan sanda, (DPO), SP Kazeem Solotan, ya tara jami’ansa inda suka kai farmaki a wajen da aka ce ana noman haramtacciyar tabar inda kuma suka sami nasarar cafke mutanan tare da tabar a hannun su.

“Binciken farko ya nuna cewa mutanan da aka Kaman suna da makeken fil ne a cikin dajin inda suke shuka haramtacciyar tabar a duk shekara,” in ji Oyeyemi.

Ya bayyana cewa, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar, Bshir Makama, ya yi umurni da a hanzarta mika mutanan zuwa sashen binciken masu aikata laifuka da binciken sirri na rundunar domin a tsananta bincike.

Oyeymi ya jiwo Makama na yaba wa al’umma a kan yanda suke kai rahotannin sirrin da suka kai ga kama wadanda ake zargin.

Ya kara da cewa, Kwamishinan ‘yan sandan ya yi umurni da a gudanar da cikakken bincike, wanda zai kai jami’an tsaro har zuwa ga gonar da ake shuka haramtacciyar tabar ta Wiwi ba tare da wani jinkiri ba.

Exit mobile version