Hukumomin tsaro a ƙasar Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargin mata da kuma mahaifiyar ƙasurgumin ɗan bindiga, Ado Aliero da ake nema ruwa a jallo a Nijeriya.
An kama matan ne a birnin Madina, inda ake zargin suna zaune ta hanyar amfani da sunayen bogi.
- DSS Ta Cafke Ɗan Bindiga Yayin Da Yake Shirin Tafiya Aikin Hajji A Sakkwato
- ’Yansanda Sun Kama Wani Mutum Sanye Da Kayan Mata A Coci A Adamawa
Majiyoyi sun bayyana cewa kama su ya biyo bayan haɗin gwiwar jami’an tsaron Saudiyya da na Nijeriya.
Wani jami’in tsaro ya ce kama su babbar nasara ce wajen karya alkadarin Ado Aliero.
Haka kuma, kamen nasu zai taimaka wajen samun bayanai game da yadda yake tafiyar da harkokinsa, inda yake samun kuɗi da kuma yadda yake gudanar da ayyukansa a ƙetare.
Ado Aliero ya shahara wajen kai hare-hare, sace mutane da kashe-kashe a Jihar Zamfara da wasu sassan Arewa Maso Yammacin Nijeriya.
An daɗe ana nemansa ba a samu nasarar kama shi ba, saboda ƙungiyarsa na da haɗin kai da goyon baya daga wurare da dama.
Ko da yake hukumomin Saudiyya ba su tabbatar da sunayen matan da aka kama ba, amma jami’an leƙen asirin Nijeriya sun ce matan na da muhimmanci wajen binciken hanyoyin samun kuɗaɗe da tallafin da ‘yan ta’adda ke samu.
Wani masani kan yaƙi da ta’addanci ya ce wannan ci gaba ya ƙara bayyana yadda matsalar tsaro a Nijeriya ta fara ɗaukar salo na ƙasa da ƙasa.
Ya kuma bayyana irin yadda ƙungiyoyin ‘yan ta’adda daga Nijeriya ke da tasiri har zuwa ƙasashen waje.
A yanzu haka, hukumomin tsaron Nijeriya da na Saudiyya na aiki tare wajen yin bincike, tare da fatan hakan zai taimaka a a kawo ƙarshen ƙungiyar Ado Aliero gaba ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp