An kama mutane huɗu da ake zargin suna haƙar ma’adanai ba tare da izini ba, tare da wani da ake zargi da sayen ma’adanan, a Minna, babban birnin Jihar Neja.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa gwamnatin Jihar Neja tare da haɗin gwiwar Hukumar Tsaro ta NSCDC sun sanya tsark a wuraren da ake haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin jihar, lamarin da ya kai ga kama mutane da dama a baya-bayan nan.
- Gwamnatin Tarayya Ba Ta Soke Jarabawar WAEC Da NECO Ba
- Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
A cewar mai magana da yawun Ma’aikatar Ma’adanai, Dibie Maureen, an kama mutanen ne yayin wani samame da aka kai wasu wuraren haƙar ma’adanai kusa da 3 Arm Zone.
Dibie ta ƙara da cewa Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Yunusa Nahauni, ne ya jagoranci wannan aikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp