Rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya, Abuja sun kama Hashiru Baku, wanda ake zargi da shirya kisan tsohon Birgediya Janar Harold Udokwere mai ritaya.
An kashe Janar Udokwere lokacin da wasu ‘yan fashi suka kai hari gidansa a ranar 22 ga watan Yuni, 2024, inda aka sace bindigarsa.
- Gwamnatin Matawalle Ce Ta Rura Wutar Ta’addanci A Arewa – Turji
- Jihar Kano Na Shirin Gudanar Da Zaben Ƙananan Hukumomi – Gwamna Abba
A ranar 24 ga watan Yuni, 2024, ‘yansanda sun kama tare da bayyana wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a kisan nasa— Ibrahim Rabiu, Nafiu Jamil, Aliyu Abdullahi, da Mohammed Nuhu.
Kwamishinan ‘yansandan Abuja, Bennett Igweh, ya bayyana cewa an kama Baku a Jihar Kano yana kokarin tserewa daga kasar.
An ce Baku ya tsere daga gidan yari na Kuje, bayan wani harin da aka kai wa gidan yarin a baya.
Kwamishina Igweh ya jaddada cewa ‘yansanda sun karbe bindigar da aka sace a gidan Janar din, agogonsa, da kuma wasu kayan matarsa.
Duk da ya tsere daga gidan yari, an zargi Baku da ci gaba da aikata laifuka.
‘Yansanda kuma sun gano kwayoyi a gidan Baku, wanda suka ce ana amfani da su domin aikata laifuka.
Ana sa ran za a ci gaba da samun karin bayani game da bincike da kuma tuhume-tuhume da za a yi masa.