Alhazai na kammala aikin hajji a rana ta uku bayan jifan shaiɗan, sannan sun gabatar da ɗawafin na karshe da ake wa laƙabi da ɗawafin ibada
Aikin jifan da aka yi na kwanaki uku a Mina, wani wurin da ke wajen Makka, na daga cikin ibadun ayyukan Hajji na ƙarshe da ke nuni da aikin Hajji ya zo karshe.
- Yadda Jami’an Saudiya Da Nijeriya Suka Yi Rangadin Wuraren Aikin Hajji
- Darussan Hadisin Aikin Hajjin Manzon Allah (SAW)
Ana fara jifan ne kwana guda bayan da mahajjata suka gabatar tsayuwar Arfa wanda daga nan suka isa Muzdhalifa, washe gari kuma aka fara gabatar da ibadar jifan.
Kwanaki na ƙarshe na aikin Hajji ya zo daidai da lokacin da Musulmi a faɗin duniya ke gudanar da bukukuwan Sallah Idi babba, wanda ke nuna farin cikin da kuma yanka dabbar da aka umarta domin yin layya.
Da fatan Allah ya karɓi ibadun mahajjatan da kuma wanda suna yi layya.