Mukthar Yakubu" />

An Kammala Daukar Fim Din ‘Ashe Za Mu Ga Juna’

A daidai lokacin da ake ganin masana’antar finafinai ta Kannywood ta shiga wani yanayi na rashin kasuwa wanda har ta kai ga yana da wahala ka ga mutum ya zuba kudinsa a cikin harkar fomin yin fim sai ga shi Hannatu Bashir mai kamfanin HANAN SYNERGY CONCEPT LTD ta shirya wani sabon fim wanda aka gama aikinsa a cikin watan Yulin da ya gabata.

Fim din mai suna ‘ASHE ZA MU GA JUNA’ ba karamin fim ba ne domin kuwa ya lashe miliyoyin kudi a wajen aikin nasa, don haka ne ma ya zama babban labari a masana’antar finafinai ta Kannywood.

Fim din dai ya samu kayan aiki na zamani wanda hakan ya bambana shi da sauran finafinai, sannan kuma duk wani jarumi da ake ji da shi a harkar fim to ya aka rawa a cikin fim cin. Jarumai irin su Ali Nuhu, Hadiza Aliyu Gabon, Umar M. Sharif, Hannatu Bashir, Salisu S. Fulani, Abbas Sadik, El-Mu’az Birniwa da sauransu.

Matashin Darakta Isah Alolo mun tambayi Hannatu Bashir dalilin ta na yin wannan fim din a daidai wannan lokacin da ake gani idan an zuba kudi a fim ba sa dawowa amma ita ta zuba miliyoyin kudi ko mene ne manufarta? Sai ta ce, “To ita harka ta kasuwa tana bukatar ka inganta kayanka kuma duk lalacewar kasuwa idan ka yi abu mai inganci za a saya, don haka ni na yarda da ingancin kayana don haka kasuwa ba z ata ba ni tsoro ba.”

Ta ci gaba da cewa, “Ni ba sabuwar shiga ba ce a harkar fim tun ina matsayin jaruma har na samu jarin da nake yin nawa na kaina ku ma na yi finafinai masu yawa, don haka na san yadda kasuwancin yake. Kawai ka yi abu mai kyau shi ne zai sa a saya.”

Ta kara da cewa, “Shi wannan fim din ASHE ZA MU GA JUNA tun daga labarinsa sai da muka tabbatar da ingancinsa don haka ma muka yi tunanin irin kayan aikin da za mu yi amfani da su da kuma jaruman da za su yi akin kai har ma wajen da za mu yi aikin da kuma tsaown lokacin da za mu dauka.”

A game da labarin kuwa cewa ta yi, “Labarin ya kunshi soyayya da fadakarwa, domin yana yin hannunka mai sanda ne game da soyayyar da maza da mata suke yi a soshiyal me midiya, wadda take kaiwa ga mawuyacin hali da matasa suke samu kansu a salon yaudara kuma in ta zo da karar kwana a har ta kai ga an rasa rai, sai kuma nuna muhimmancin kula da tarbiyyar yara a wannan lokacin musamman ‘ya’ya mata wadanda su ne aka fi ruda da abin duniya.”

Ana sa ran dai nan gaba kadan fim din zai shiga kasuwa, amma kafin shigarsa za a fara kallon sa a satin Sallah a garin Kaduna kamar yadda furodusan fim din Hannatu Bashir ta shaida mana.

Exit mobile version