Da safiyar jiya Lahadi bisa agogon wurin, aka kammala horon hadin gwiwa tsakanin sojojin saman kasashen Sin da Masar mai suna “Shaho na wayewar kai-2025” cikin nasara, a wani sansanin sojojin saman Masar, wanda ya kwashe kwanaki guda 18.
Wannan horon na hadin gwiwa shi ne karo na farko da rundunar sojin saman kasar Sin ta aike da dakaru zuwa kasashen Afirka domin ba da horon hadin gwiwa. A yayin horon na hadin gwiwa, sojojin saman kasashen Sin da Masar sun tattauna tare da yin musayar ra’ayi kan nau’o’in horarwa, da dabarun yaki da jiragen sama, da samar da man fetur a sama da dai sauransu, kuma sun samu nasarar kammala horarwa kan ayyukan sarrafa jiragen sama, da kiyaye tsaron sararin sama, da ceton mutane a fagen yaki, da yin darussan hadin gwiwa da dai sauransu, wannan wani mafari ne da kuma ci gaba a kan hanyar hadin gwiwar soji tsakanin kasashen biyu. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp