Ibrahim Muhammad" />

An Karrama Sarkin Butalawa Bisa Hidima Ga Al’umma

An yi kira ga Gwamnati ta baiwa masu unguwanni,dakatai da hakimai goyon baya wajen rufa musu baya a kokarinda ake na kauda shaye-shaye da miyagun laifuka a tsakanin matasa.

Sarkin Butalawa,kuma Daraktan shiyya mai kulada Asibitocin Waziri Gidado dana Mariya Sunusi dana Dawanau a jahar Kano.Alhaji Kabiru Salisu Butalawa ya bayyana haka a wajen taron fadakarwa akan illar shan kwayoyi da karramawa ga wasu zababbun mutane kan hidimtawa al’umma da “Salka Media” ta yi a Kano.

Ya ce idan Gwamnati bata basu goyon baya dayakamata ba,sai a sami wani dan siyasa ko yaronsa a cikin irin wannan hali da ba’aso sai kaga yafi karfin a hukuntashi saboda daurin gindi.

Sarkin na Butalawa Alhaji Kabiru Salisu ya ce idan iyayen kasar zasu sami cikakkayar goyon bayan hukuma duk abinda zasu iyayi wajen kauda harkar shaye- shaye da miyagun dabi’oi  zai kai ga nasara da taimakon Ubangiji.

Sarkin yayi nuni da cewa a garinsa na Butalawa akwai irin wannan kwamitoci a kowace unguwa kama daga na kula da tsaro hana shaye-shaye da taimakawa marayu da ilimi,wanda yanzu takai da wuya kaga an kai wani gaban yansanda akan aikata wani abu ba daidai ba a garin saboda irin  dakile ayyukan bata gari da suke gudanarwa.

Ya kara da cewa irin wadannan Kwamitoci a garin Butalawa suna taimakawa cigaban marayu ta mayar dasu makaranta da tallafawa igaban karatunsu hakan tasa yawan marayu a garin suna kokarin yin karatu.

Daraktan Shiyya mai kulada Asibitocin Waziri Gidado,Mariya Sunusi dana Dawanau.Alhaji Kabiru Salisu ya ce karramawarda da akayi masa zai kara masa kwarin gwiwa akan sauke nauyin  aikinsa da yake tsakani da Allah bai sani ba ashe ana lura da abinda yake kuma aka zabo shi aka karramashi akai.

Sarkin ya ce wannan aiki na Gwamnati da yake da hidimar al’ummar ta sauke nauyin sarauta karramawar yana fata ta kara masa dama tayin aiki tukuru ga cigaban al’ummar kano.

A yayin taron dai an karrama sarkin na Butalawa Alhaji Kabiru Salisu da Ratayen Sisin gwai da takardar shaida ta yabo da Garkuwa.

Exit mobile version