Kungiyar Matasan ‘Yan Jarida reshen jihar Kaduna ta karrama Shugabar Kungiyar reshen jihar Hajiya Asma’u Yawo Aliyu da babbar lambar yabo bisa kokarinta na samar da ci gaban Kungiyar reshen jihar.
Lambar yabon ta 2022, an ba ta ne, musamman a kan sauyin ci gaba da ta samar a cikin watanni goma da hawanta Karagar shugabancin Kungiyar.
Shugaban da ya hada taron Basheer Musa ya ce, Asma’u ta zama wacce tafi cancanta da lashe babbar lambar yabon, biyo bayan zaben da Kungiyar ta gudanar a kafar yanar Gizo.
Da take yin godiya bisa karramar, Asma’u ta ce, hakan zai kara mata kaimi wajen jajirce wa don gudanar da shugabanci na gari ga ‘ya’yan Kungiyar reshen jihar.