Zubairu M Lawal">

An Karrama Uwargidan Gwamnan Nasarawa Da Sarautar Jarumar Nku

Masarautar Unguwar Makama da a ke yi wa lakabi da Masarautan Nku da ke karamar hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa ta karrama Uwargidan Gwamna Nasarawa, Hajiya Silifat Abdullah Sule, da sarautar Jarumar Nku.

Yayin da ta ke godiya wajen karban Sarautan Uwargidan Gwamnan Hajiya Silifat Abdullah Sule ta yabawa al’umman yankin Uwangar Makama saboda yadda suka rungumi akidar zaman lafiya a yankin.
Hajiya Silifat Abdullah Sule ta ce al’umman kauyen yunku sun zamo abin koyi ga al’umman jihar Nasarawa saboda yadda mazauna garin suka rungumi tafarkin zaman lafiya da kowata kabila dake rayuwa a tare dasu.
Hajiya Silifat Abdullah Sule ta ce akidar ta na taimakawa matan jihar Nasarawa da takeyi wanda ya sanya kungiyoyin mata a jihar suke amfana da Gwamnatin Injiniya Abdullah Sule wajen more rayuwar mulkin Demukurdiyya za ta cigaba da yi.
Ta ce Babban burin ta a wannan Gwamnatin taga ana gudanar da abubuwan amfani a cikin jihar Nasarawa tare da mata.
Saboda mata suna bada lokaci wajen zaber Gwamnati kuma tana da burin taga mata sunyi bankwana da matsalolin rayuwa.
Hajiya Silifat Abdullah Sule tayi kira ga kungiyoyin matan jihar Nasarawa dasu cigaba da fadakar da matan jihar su mike tsaye wajen koyon sana’o’i na dogaro da kai.
Ta ce Gwamnatin Injiniya Abdullah Sule tana iya kokari wajen taimakawa Matan Jihar Nasarawa da abubuwan sana’o’i da koyar da su da kuma basu jali saboda dogaro da kai.
Hajiya Silifat tace Gwamnatin Injiniya Abdullah Sule tana da bukatar sauya fasalin matan jihar Nasarawa saboda su zamo abin koyi ga Matan wasu jihohin.
Ta kara da cewa har wayau ta na kara kira ga mata dasu zama masu wayewa da sanin hakokinsu kuma wannan Gwamnatin ba za ta zura ido ta kyale duk wanda zai ci zarafin mata a wannan Jihar ba.
Hajiya Silifat ta taimakawa matan kungiyoyin da ke Masarautan Nku da tallafin kudi Naira miliyan daya.
Da take mai da jawabi  Shugaban kungiyar matan Masarautan Madan Habila Adamu Aboki ta yabawa Uwargidan Gwamnan Hajiya Silifat Abdullah Sule saboda kokarin da ta ke yi na cigaban Matan Jihar Nasarawa.
Ta ce zuwan Gwamnatin Injiniya Abdullah Sule mata sun amfana a fannoni dabam dabam. Kuma tallafin da Uwargidan Gwamnan take badawa domin gina Matan Jihar Nasarawa ya shiga ko ina ana ji a fadin kasan nan.
Madam Habila Adamu Aboki ta jin jinawa Hajiya Silifat Abdullah Sule da kuma kara nuna goyon baya ga Gwamnatin Abdullah Sule saboda yadda Gwamnatin ta samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin Jihar Nasarawa.

Exit mobile version