Idris Aliyu Daudawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

An Karya Lagon Boko Haram – Fadar Shugaban Kasa

by Idris Aliyu Daudawa
January 16, 2021
in RAHOTANNI
4 min read
, Idris Bello
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A daidai lokacin da Nijeriya tayi bikin tunawa da ‘yan mazan jiya ko abinda aka fi ranar tunawa da sojoji wadanda suka kwanta dama, na shekarar 2021 ranar juma’ar makon daya gabata fadar Shugaban kasa ta bayyana cewar yanzu ‘yan kungiyar Boko Haraman karya masu lago basu da karfi kamar a shekarar 2015.

Wannan kuwa ya biyo bayan ganin karshen wasu ‘yan tadda wadanda suka wuce 2,403 wadanda suka hada da duk masu aikata laifuka daban- daban, kamar ‘yan’ta’adda, masu garkuwa da jama’a, da sojoji suka yi maganin su, a sanadiyar matakan gamawa da su daban- daban tsakanin watannin 18 na watan Maris da kuma 30 ga watanDisamba na shekarar data gabata ta 2020. Wannan ya hada da ‘yan ta’addar da aka kashe masu yawa da aka kashe lokuttan da aka rika kai masu hare- hare ta sama.

Shi dai bikin an yi shi ne da safe ranar Litinin 11 ga watan Janiru a National Arcade,daura da  Eagles Skuare,abinda aka fisani da suna Three Arms Zone, Abuja.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman akan watsa labarai da hulda da jama’a Femi Adesina, shi ne wanda ya bayyana haka a wani bayanin da ya yi ma taken “Halin da al’amarin tsaro yake lokacin da Nijeriya take bikin tunawa da sojoji’yan mazan jiya wadanda suka kwanta dama wanda fadar shugaban kasa ta shirya, da hakan ne kuma aka bayyana cigaban da kuma nasarorin da aka samu ta bangaren tsaro, a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Dangane kuma da tsaron cikin gida, Adesina ya jaddada cewar ‘yan kungiar Boko Haram basu da wani karsashi kamar yadda suke a shekarar 2015.”

Adesina domin ya tabbatar da bayanan da ya yi ya yi, amfani da wata maganar da gwamnan jihar Borno Babagana Zulum wadda ya yi ranar 2 ga watan Disamba 2020, duk da yake wasu abubuwa sun faru na tada hankali a jihar, amma hakan ita jihar da kuma sashen na Arewa masu gabas, da akwai bambanci har yanzu a cikin wannan mulkin da ake ciki..

“Bugu da kari kuma sojoji sun kubutar da jimillar mutane 864 wadanda aka yi garkuwa dasu awurare daban- daban na fadin tarayyar Nijeriya.

“Hakanan ma an kwato litar main a gas 9,684,797 da kuma lita 33,516,000 ta kananzir.

“Kazalika ma an kama masu aikata laifuka 1,910 inda kuma aka same su tare da manyan makamai, da kuma albarusa a lokacin.

Ya kara jaddada cewar “An samu kwato gangar danyen mai 46,581.8 da kuma litar man fetur 22,881,257 wadda sojoji suka kwato.”

Hakanan ma a wani abinda ake kira cigaba tsakanin watannin Maris da Disamba 2020 Adesina ya bayyana cewar an samu wani karin ci gabaa sashen Arewa maso yamma inda aka kwato dabbobi, 5,281, sai kuma albarusai 6,951da kuma manyan bindigogi 120 daga hannun ‘yan ta’adda.

Ya kara da cewa, “a cikin wannan, an kama mutane 79 da suka hada da masu matukar amfani,” A yankin na Arewa ta tsakiya, Adesina ya baytyana cewa sojojin na Safe Haben, Whirl Stroke da kuma Thunder Strike sun ceto jimillar wadanda aka yi garkuwa da su, da bindigogi daban-daban guda105 da kuma harsasai 513 da shanu 1,055 da aka kwato daga hannun ‘yan bindiga da sauran masu aikata muggan laifuka. a cikin Yankin. Ya kara da cewa an kama masu laifi 1,250, ciki har da dangin Darul Salam, a lokacin, da sojoji suka kashe jimillar ‘yan bindiga 125 da suka hada da shugabannin kungiyoyin’ yan bindiga.

 

A Kudu maso kudu kuma mataimakin shugaban kasa na musamman a harkar watsa labarai da hulda da jama’a ya bayyana cewar sojojin operation Delta safe sun damke lita man fetur 8,890,300 da kuma litar mai 33, 516, 00 ta man gas. Ya kara da cewa, “Dakarun sun hana wasu matatun mai guda 185 wadanda suke  ba bisa ka’ida ba, rami 85 da kuma tankunan karafa 163 duk a wannan lokacin.

Bugu da kari kuma sojojin sun haka jimillar ganga 31,236.8 ta danyen mai da aka sata da kuma lita 12,272,652 ta mai daga yankin barayin mai. “Hakanan ma an ceto jimillar mutane 47 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kame masu aikata laifi 72 da masu laifi.

“An samu jimllar buhuna 4,250 masu nauyin kilogiram 50 na kasar waje da aka shigo da shinkafar ta fasakwauri suka kame kwale-kwale 45 da ke aikata haramtattun ayyukac dasu.”Sojojin sun kuma kama jimillar ‘yan fashi 53 da manyan motoci 25 tare da kwato bindigogi 23, da albarusai 65,330 da kuma lalata sansanonin’ yan fashin teku 23.

“Shiyyar Kudu maso yamma kuma Adesina ya bayyana cewar sojojin Operation Awatse a yankin tsakanin 18 ga Maris da kuma 30 ga Disamba, 2020 sun samu sa’ar damke jimillar LMS 10,458,600 ta man fetur; ganga 15,345 na satar danyen mai da lita 345,000 na gas da aka sata. “Bugu da kari kumasojojin sun kwato jimllar harsasai 3,594 da bindigogi iri-iri 14. Har ila yau kuma a cikin wannan lokacin, jimillar wurare 23 na haramtattun matatun ba su da hurumi, yayin da aka kame kwale-kwale 15 da manyan motoci 23 da ke aikata haramtattun ayyuka dasu.

Daga karshe kuma, a tsakanin lokacin an kubutar da mutane 35 wadanda aka yi garkuwa da su yayin da kumk aka kame 48kamar yadda Adesina ya bayyana. Shugaba Muhammadu Buhari; Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo; Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan; Kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Femi Gbajabiamiala; da Babban Jojin Nijeriya, Tanko Muhammadu, shugabannin hafsoshi soja ,da kuma babban sufeton ‘yan sanda na daga cikin wadanda suka sanya fure don girmama sojojin da suka kwanta dama.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Muhimmancin Yin Gwajin Kwayar Halitta Kafin Aure

Next Post

Gobara Ta Yi Sanadiyyar  Mutuwar Uwa Da ‘Ya’yanta Biyu A Kirfi

RelatedPosts

Tuhumar Malam Abduljabbar Za A Yi, Ba Mukabala Da Shi Ba– Sheikh Khalil

by Idris Aliyu Daudawa
9 hours ago
0

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja Shugaban Majalisar Malamai na Shiyyar...

ISWAP

Boko Haram Ta Yi Garkuwa Da Ma’aikatan Jinkai Bakwai A Dikwa

by Idris Aliyu Daudawa
10 hours ago
0

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri A harin bayan nan da mayakan...

Makanike

Shari’ar Gonaki: Kotu Ta Aike Wa Rundunar Soja Da Ma’aikarar Shari’a Sammaci

by Idris Aliyu Daudawa
10 hours ago
0

Daga Isa Abdullahi Gidan ‘Bakko, Zariya Kotun daukaka kara dake...

Next Post
Gobara Ta Yi Sanadiyyar  Mutuwar Uwa Da ‘Ya’yanta Biyu A Kirfi

Gobara Ta Yi Sanadiyyar  Mutuwar Uwa Da ‘Ya’yanta Biyu A Kirfi

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version