An gudanar da taron kwararru da masu tsara manufofi, game da hadin gwiwar Sin da kasashen nahiyar Afirka a jiya Alhamis, inda masu gabatar da jawabai suka yi kira, game da bukatar daga matsayin alakar sassan biyu zuwa sabon mataki.
Taron wanda ya gudana karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Afirka AU, a birnin Addis Ababan kasar Habasha, ya hallara jami’ai daga hukumar gudanarwar kungiyar AU, da jakadu daga kasashen Afirka, da takwarorinsu na kasar Sin dake kasashe mambobin kungiyar, da malaman jami’o’i, da kwararru da dai sauransu.
Da yake tsokaci yayin taron, kwamishinan AU mai lura da ilimi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire Mohammed Belhocine, ya ce kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen cimma nasarar aiwatar da manufofin hadin gwiwa da hukumar zartaswar AU, da ma kasashe mambobin kungiyar, musamman karkashin dandalin raya hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na FOCAC.
Kaza lika Mr. Belhocine, ya bayyana fatansa na ganin an ci gaba da fadada hadin gwiwa tsakanin sassan biyu a karin wasu fannoni.
Shi ma shugaban ofishin wakilcin Sin a kungiyar AU Hu Changchun, jaddada kamalan Belhocine ya yi, yana mai cewa, AU ta yi rawar gani wajen tabbatar da nasarar kudurorin raya tattalin arziki, zamantakewa da ci gaban siyasar al’ummun Afirka.
Hu ya ce cikin manyan manufofin diflomasiyyar kasar Sin, akwai dora muhimmancin gaske ga karfafa goyon baya da hadin gwiwa da kasashen Afirka. (Saminu Alhassan)